Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 15 - Al-Hijr
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Hijr 15:1
L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa
Verse 2 — Surah Al-Hijr 15:2
Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi
Verse 3 — Surah Al-Hijr 15:3
Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani
Verse 4 — Surah Al-Hijr 15:4
Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne
Verse 5 — Surah Al-Hijr 15:5
Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba
Verse 6 — Surah Al-Hijr 15:6
Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne
Verse 7 — Surah Al-Hijr 15:7
Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya
Verse 8 — Surah Al-Hijr 15:8
Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,* bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba
Verse 9 — Surah Al-Hijr 15:9
Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi
Verse 10 — Surah Al-Hijr 15:10
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka
Verse 11 — Surah Al-Hijr 15:11
Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi
Verse 12 — Surah Al-Hijr 15:12
Kamar wancan ne Muke shigar da shi* a cikin zukãtan mãsu laifi
Verse 13 — Surah Al-Hijr 15:13
Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige)
Verse 14 — Surah Al-Hijr 15:14
Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa
Verse 15 — Surah Al-Hijr 15:15
Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce
Verse 16 — Surah Al-Hijr 15:16
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo
Verse 17 — Surah Al-Hijr 15:17
Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa
Verse 18 — Surah Al-Hijr 15:18
Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi
Verse 19 — Surah Al-Hijr 15:19
Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli
Verse 20 — Surah Al-Hijr 15:20
Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã* da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba
Verse 21 — Surah Al-Hijr 15:21
Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne
Verse 22 — Surah Al-Hijr 15:22
Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba
Verse 23 — Surah Al-Hijr 15:23
Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada
Verse 24 — Surah Al-Hijr 15:24
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri
Verse 25 — Surah Al-Hijr 15:25
Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani
Verse 26 — Surah Al-Hijr 15:26
Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja
Verse 27 — Surah Al-Hijr 15:27
Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar* iskar zafi
Verse 28 — Surah Al-Hijr 15:28
Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja
Verse 29 — Surah Al-Hijr 15:29
To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa* a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada
Verse 30 — Surah Al-Hijr 15:30
Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya
Verse 31 — Surah Al-Hijr 15:31
Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar
Verse 32 — Surah Al-Hijr 15:32
Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba
Verse 33 — Surah Al-Hijr 15:33
Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja
Verse 34 — Surah Al-Hijr 15:34
Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne
Verse 35 — Surah Al-Hijr 15:35
Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako
Verse 36 — Surah Al-Hijr 15:36
Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su
Verse 37 — Surah Al-Hijr 15:37
Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri
Verse 38 — Surah Al-Hijr 15:38
Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne
Verse 39 — Surah Al-Hijr 15:39
Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya
Verse 40 — Surah Al-Hijr 15:40
Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake
Verse 41 — Surah Al-Hijr 15:41
Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici
Verse 42 — Surah Al-Hijr 15:42
Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu
Verse 43 — Surah Al-Hijr 15:43
Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya
Verse 44 — Surah Al-Hijr 15:44
Tanã da ƙõfõfi bakwai,* ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe
Verse 45 — Surah Al-Hijr 15:45
Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa
Verse 46 — Surah Al-Hijr 15:46
Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu
Verse 47 — Surah Al-Hijr 15:47
Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã
Verse 48 — Surah Al-Hijr 15:48
Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba
Verse 49 — Surah Al-Hijr 15:49
Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai
Verse 50 — Surah Al-Hijr 15:50
Kuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi
Verse 51 — Surah Al-Hijr 15:51
Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm
Verse 52 — Surah Al-Hijr 15:52
A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne
Verse 53 — Surah Al-Hijr 15:53
Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani
Verse 54 — Surah Al-Hijr 15:54
Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra* ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara
Verse 55 — Surah Al-Hijr 15:55
Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni
Verse 56 — Surah Al-Hijr 15:56
Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu
Verse 57 — Surah Al-Hijr 15:57
Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni
Verse 58 — Surah Al-Hijr 15:58
Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi
Verse 59 — Surah Al-Hijr 15:59
Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya
Verse 60 — Surah Al-Hijr 15:60
Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka
Verse 61 — Surah Al-Hijr 15:61
To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu
Verse 62 — Surah Al-Hijr 15:62
Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba
Verse 63 — Surah Al-Hijr 15:63
Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa
Verse 64 — Surah Al-Hijr 15:64
Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne
Verse 65 — Surah Al-Hijr 15:65
Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku
Verse 66 — Surah Al-Hijr 15:66
Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba
Verse 67 — Surah Al-Hijr 15:67
Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra
Verse 68 — Surah Al-Hijr 15:68
Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni
Verse 69 — Surah Al-Hijr 15:69
Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki
Verse 70 — Surah Al-Hijr 15:70
Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba
Verse 71 — Surah Al-Hijr 15:71
Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna* idan kun kasance mãsu aikatãwa ne
Verse 72 — Surah Al-Hijr 15:72
Rantsuwa da* rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa
Verse 73 — Surah Al-Hijr 15:73
Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã
Verse 74 — Surah Al-Hijr 15:74
Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu
Verse 75 — Surah Al-Hijr 15:75
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali
Verse 76 — Surah Al-Hijr 15:76
Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya
Verse 77 — Surah Al-Hijr 15:77
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni
Verse 78 — Surah Al-Hijr 15:78
Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika* sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci
Verse 79 — Surah Al-Hijr 15:79
Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani
Verse 80 — Surah Al-Hijr 15:80
Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri* sun ƙaryata Manzanni
Verse 81 — Surah Al-Hijr 15:81
Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su
Verse 82 — Surah Al-Hijr 15:82
Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu
Verse 83 — Surah Al-Hijr 15:83
Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba
Verse 84 — Surah Al-Hijr 15:84
Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba
Verse 85 — Surah Al-Hijr 15:85
Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau
Verse 86 — Surah Al-Hijr 15:86
Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani
Verse 87 — Surah Al-Hijr 15:87
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu* da Alƙur'ãni mai girma
Verse 88 — Surah Al-Hijr 15:88
Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni
Verse 89 — Surah Al-Hijr 15:89
Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne
Verse 90 — Surah Al-Hijr 15:90
Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa
Verse 91 — Surah Al-Hijr 15:91
Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi
Verse 92 — Surah Al-Hijr 15:92
To, rantsuwa da Ubangijinka!* Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya
Verse 93 — Surah Al-Hijr 15:93
Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa
Verse 94 — Surah Al-Hijr 15:94
Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki
Verse 95 — Surah Al-Hijr 15:95
Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu* izgili
Verse 96 — Surah Al-Hijr 15:96
Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani
Verse 97 — Surah Al-Hijr 15:97
Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili)
Verse 98 — Surah Al-Hijr 15:98
Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada
Verse 99 — Surah Al-Hijr 15:99
Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka