Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi* daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa
Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai
Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni
Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta
Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa
Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa,* sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba
Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai
Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa
Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa
Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta
Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance
Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãnin hisu su yi tunãni
Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba
Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai
Kuma sunã sanya rabõ *ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa
Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana
Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu,* dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba
Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta)
Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni
Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre
Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã
Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye* da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta
Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni
Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi
Kuma Allah Ya fifita sãshenku* a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu
Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta
Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba
Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici
Kuma ga Allah gaibin* sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne
Shin ba su ga tsuntsãye* ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni
Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu* da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci
Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna *sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa
Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba
Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne
Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi)
Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa
Kuma ku cika da alkãwarin* Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa
Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna
Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa
Kada ku riƙi rantsuwõyin ku dõmin yaudara a tsakãnin ku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma
Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa
Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa
Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ã'a, mafi yawansu bã swa sani
Ka ce: "Rũhul ¡udusi* ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma (dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi
Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai
A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba
Kuma Allah Ya buga misãli,* wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa
Abin sani kawai (Allah) Ya haramta* muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai
Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba
Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni,* kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki* da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai
Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa.* Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã
Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima* da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa
Kuma idan kuka sãka* wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri
Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci