Back to Languages

Hausa - Chapter 24 - An-Nur

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 39 — Surah An-Nur 24:39

Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi* Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne