Back to Languages

Hausa - Chapter 50 - Qaf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Qaf 50:1

Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma

Verse 2 — Surah Qaf 50:2

Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki

Verse 3 — Surah Qaf 50:3

Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa

Verse 4 — Surah Qaf 50:4

Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littãfi mai tsarẽwa

Verse 5 — Surah Qaf 50:5

Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa

Verse 6 — Surah Qaf 50:6

Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi

Verse 7 — Surah Qaf 50:7

Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa

Verse 8 — Surah Qaf 50:8

Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali

Verse 9 — Surah Qaf 50:9

Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa

Verse 10 — Surah Qaf 50:10

Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna

Verse 11 — Surah Qaf 50:11

Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake

Verse 12 — Surah Qaf 50:12

Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, *da Samũdãwa

Verse 13 — Surah Qaf 50:13

Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu

Verse 14 — Surah Qaf 50:14

Da ma'abũta ƙunci *da mutãnen Tubba'u,** kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata

Verse 15 — Surah Qaf 50:15

Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa

Verse 16 — Surah Qaf 50:16

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayẽnsa

Verse 17 — Surah Qaf 50:17

A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne

Verse 18 — Surah Qaf 50:18

Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce

Verse 19 — Surah Qaf 50:19

Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa

Verse 20 — Surah Qaf 50:20

Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa

Verse 21 — Surah Qaf 50:21

Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida

Verse 22 — Surah Qaf 50:22

(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne

Verse 23 — Surah Qaf 50:23

Kuma abõkin haɗinsa* ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce

Verse 24 — Surah Qaf 50:24

(A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai

Verse 25 — Surah Qaf 50:25

Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka

Verse 26 — Surah Qaf 50:26

Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani

Verse 27 — Surah Qaf 50:27

Abõkin haɗinsa* ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa

Verse 28 — Surah Qaf 50:28

Ya ce: "Kada ku yi husũma a wur Nalhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku

Verse 29 — Surah Qaf 50:29

Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyi Na

Verse 30 — Surah Qaf 50:30

Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,* akwai wani ƙãri

Verse 31 — Surah Qaf 50:31

Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba

Verse 32 — Surah Qaf 50:32

Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa)

Verse 33 — Surah Qaf 50:33

Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, *kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali

Verse 34 — Surah Qaf 50:34

(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, *waccan ita ce rãnar dawwama

Verse 35 — Surah Qaf 50:35

Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima

Verse 36 — Surah Qaf 50:36

Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?* (Babu)

Verse 37 — Surah Qaf 50:37

Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa)

Verse 38 — Surah Qaf 50:38

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba

Verse 39 — Surah Qaf 50:39

Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi* game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta

Verse 40 — Surah Qaf 50:40

Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada

Verse 41 — Surah Qaf 50:41

Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri *makusanci

Verse 42 — Surah Qaf 50:42

Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari)

Verse 43 — Surah Qaf 50:43

Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take

Verse 44 — Surah Qaf 50:44

Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu

Verse 45 — Surah Qaf 50:45

Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,* ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa