Back to Languages

Hausa - Chapter 51 - Adh-Dhariyat

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Adh-Dhariyat 51:1

Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa

Verse 2 — Surah Adh-Dhariyat 51:2

Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa)

Verse 3 — Surah Adh-Dhariyat 51:3

Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi

Verse 4 — Surah Adh-Dhariyat 51:4

Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah)

Verse 5 — Surah Adh-Dhariyat 51:5

Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne

Verse 6 — Surah Adh-Dhariyat 51:6

Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne

Verse 7 — Surah Adh-Dhariyat 51:7

Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo)

Verse 8 — Surah Adh-Dhariyat 51:8

Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani)

Verse 9 — Surah Adh-Dhariyat 51:9

Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya)

Verse 10 — Surah Adh-Dhariyat 51:10

An la'ani mãsu ƙiri-faɗi

Verse 11 — Surah Adh-Dhariyat 51:11

Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci

Verse 12 — Surah Adh-Dhariyat 51:12

Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku

Verse 13 — Surah Adh-Dhariyat 51:13

Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su

Verse 14 — Surah Adh-Dhariyat 51:14

(A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa

Verse 15 — Surah Adh-Dhariyat 51:15

Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari

Verse 16 — Surah Adh-Dhariyat 51:16

Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya)

Verse 17 — Surah Adh-Dhariyat 51:17

Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci

Verse 18 — Surah Adh-Dhariyat 51:18

Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri

Verse 19 — Surah Adh-Dhariyat 51:19

Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo

Verse 20 — Surah Adh-Dhariyat 51:20

Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni

Verse 21 — Surah Adh-Dhariyat 51:21

Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba

Verse 22 — Surah Adh-Dhariyat 51:22

Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari

Verse 23 — Surah Adh-Dhariyat 51:23

To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana

Verse 24 — Surah Adh-Dhariyat 51:24

Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka

Verse 25 — Surah Adh-Dhariyat 51:25

A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi

Verse 26 — Surah Adh-Dhariyat 51:26

Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna

Verse 27 — Surah Adh-Dhariyat 51:27

Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba

Verse 28 — Surah Adh-Dhariyat 51:28

Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi

Verse 29 — Surah Adh-Dhariyat 51:29

Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)

Verse 30 — Surah Adh-Dhariyat 51:30

Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi

Verse 31 — Surah Adh-Dhariyat 51:31

(Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni

Verse 32 — Surah Adh-Dhariyat 51:32

Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi

Verse 33 — Surah Adh-Dhariyat 51:33

Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom)

Verse 34 — Surah Adh-Dhariyat 51:34

Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna

Verse 35 — Surah Adh-Dhariyat 51:35

Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai

Verse 36 — Surah Adh-Dhariyat 51:36

Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi

Verse 37 — Surah Adh-Dhariyat 51:37

Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi

Verse 38 — Surah Adh-Dhariyat 51:38

Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne

Verse 39 — Surah Adh-Dhariyat 51:39

Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci

Verse 40 — Surah Adh-Dhariyat 51:40

Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi

Verse 41 — Surah Adh-Dhariyat 51:41

Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu

Verse 42 — Surah Adh-Dhariyat 51:42

Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa

Verse 43 — Surah Adh-Dhariyat 51:43

Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci

Verse 44 — Surah Adh-Dhariyat 51:44

Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo

Verse 45 — Surah Adh-Dhariyat 51:45

Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba

Verse 46 — Surah Adh-Dhariyat 51:46

Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai

Verse 47 — Surah Adh-Dhariyat 51:47

Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa

Verse 48 — Surah Adh-Dhariyat 51:48

Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ

Verse 49 — Surah Adh-Dhariyat 51:49

Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni

Verse 50 — Surah Adh-Dhariyat 51:50

Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi

Verse 51 — Surah Adh-Dhariyat 51:51

Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi

Verse 52 — Surah Adh-Dhariyat 51:52

Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci

Verse 53 — Surah Adh-Dhariyat 51:53

shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai

Verse 54 — Surah Adh-Dhariyat 51:54

Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne

Verse 55 — Surah Adh-Dhariyat 51:55

Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai

Verse 56 — Surah Adh-Dhariyat 51:56

Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini

Verse 57 — Surah Adh-Dhariyat 51:57

Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni

Verse 58 — Surah Adh-Dhariyat 51:58

Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi

Verse 59 — Surah Adh-Dhariyat 51:59

To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa

Verse 60 — Surah Adh-Dhariyat 51:60

Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari