Back to Languages

Hausa - Chapter 52 - At-Tur

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah At-Tur 52:1

Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã)

Verse 2 — Surah At-Tur 52:2

Da wani littãfi rubũtacce

Verse 3 — Surah At-Tur 52:3

A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa

Verse 4 — Surah At-Tur 52:4

Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda)

Verse 5 — Surah At-Tur 52:5

Da rufin nan da aka ɗaukaka

Verse 6 — Surah At-Tur 52:6

Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa)

Verse 7 — Surah At-Tur 52:7

Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce

Verse 8 — Surah At-Tur 52:8

Bã ta da mai tunkuɗẽwa

Verse 9 — Surah At-Tur 52:9

Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo

Verse 10 — Surah At-Tur 52:10

Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa

Verse 11 — Surah At-Tur 52:11

To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 12 — Surah At-Tur 52:12

Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã

Verse 13 — Surah At-Tur 52:13

Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa

Verse 14 — Surah At-Tur 52:14

(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita

Verse 15 — Surah At-Tur 52:15

To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani

Verse 16 — Surah At-Tur 52:16

Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa

Verse 17 — Surah At-Tur 52:17

Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima

Verse 18 — Surah At-Tur 52:18

Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm

Verse 19 — Surah At-Tur 52:19

(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa

Verse 20 — Surah At-Tur 52:20

Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu

Verse 21 — Surah At-Tur 52:21

Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu *suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta

Verse 22 — Surah At-Tur 52:22

Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari

Verse 23 — Surah At-Tur 52:23

Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi

Verse 24 — Surah At-Tur 52:24

Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle

Verse 25 — Surah At-Tur 52:25

Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna

Verse 26 — Surah At-Tur 52:26

Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro

Verse 27 — Surah At-Tur 52:27

To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi

Verse 28 — Surah At-Tur 52:28

Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama

Verse 29 — Surah At-Tur 52:29

To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba

Verse 30 — Surah At-Tur 52:30

Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ

Verse 31 — Surah At-Tur 52:31

Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku

Verse 32 — Surah At-Tur 52:32

Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi

Verse 33 — Surah At-Tur 52:33

Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba

Verse 34 — Surah At-Tur 52:34

Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne

Verse 35 — Surah At-Tur 52:35

Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta

Verse 36 — Surah At-Tur 52:36

Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba

Verse 37 — Surah At-Tur 52:37

Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya

Verse 38 — Surah At-Tur 52:38

Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne

Verse 39 — Surah At-Tur 52:39

Shin, Yanã da* 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne

Verse 40 — Surah At-Tur 52:40

Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar

Verse 41 — Surah At-Tur 52:41

Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa

Verse 42 — Surah At-Tur 52:42

Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi

Verse 43 — Surah At-Tur 52:43

Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki

Verse 44 — Surah At-Tur 52:44

Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna

Verse 45 — Surah At-Tur 52:45

To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa

Verse 46 — Surah At-Tur 52:46

Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su

Verse 47 — Surah At-Tur 52:47

Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba

Verse 48 — Surah At-Tur 52:48

Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnun Mu, kuma ka tsarkake* Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu)

Verse 49 — Surah At-Tur 52:49

Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) da lõkacin jũyãwar taurãri