Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 53 - An-Najm
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah An-Najm 53:1
Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku
Verse 2 — Surah An-Najm 53:2
Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba
Verse 3 — Surah An-Najm 53:3
Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa
Verse 4 — Surah An-Najm 53:4
(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa
Verse 5 — Surah An-Najm 53:5
(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi *ya sanar da shi
Verse 6 — Surah An-Najm 53:6
Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita
Verse 7 — Surah An-Najm 53:7
Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka
Verse 8 — Surah An-Najm 53:8
Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa
Verse 9 — Surah An-Najm 53:9
Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa
Verse 10 — Surah An-Najm 53:10
Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa)
Verse 11 — Surah An-Najm 53:11
Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba
Verse 12 — Surah An-Najm 53:12
Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani
Verse 13 — Surah An-Najm 53:13
Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa
Verse 14 — Surah An-Najm 53:14
A wurin da magaryar tuƙẽwa take
Verse 15 — Surah An-Najm 53:15
A inda taken, nan Aljannar makoma take
Verse 16 — Surah An-Najm 53:16
Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta
Verse 17 — Surah An-Najm 53:17
Ganinsa* bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba
Verse 18 — Surah An-Najm 53:18
Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma* daga ãyõyin Ubangijinsa
Verse 19 — Surah An-Najm 53:19
Shin, kun ga Lãta da uzza
Verse 20 — Surah An-Najm 53:20
Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu
Verse 21 — Surah An-Najm 53:21
Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace
Verse 22 — Surah An-Najm 53:22
Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe
Verse 23 — Surah An-Najm 53:23
Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar* ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton)
Verse 24 — Surah An-Najm 53:24
Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri
Verse 25 — Surah An-Najm 53:25
To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure)
Verse 26 — Surah An-Najm 53:26
Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda
Verse 27 — Surah An-Najm 53:27
Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace
Verse 28 — Surah An-Najm 53:28
Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya
Verse 29 — Surah An-Najm 53:29
Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya)
Verse 30 — Surah An-Najm 53:30
Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya
Verse 31 — Surah An-Najm 53:31
Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau
Verse 32 — Surah An-Najm 53:32
Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa
Verse 33 — Surah An-Najm 53:33
Shin, ka ga wannan da ya jũya baya
Verse 34 — Surah An-Najm 53:34
Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa
Verse 35 — Surah An-Najm 53:35
Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin
Verse 36 — Surah An-Najm 53:36
Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã
Verse 37 — Surah An-Najm 53:37
Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari
Verse 38 — Surah An-Najm 53:38
Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani
Verse 39 — Surah An-Najm 53:39
Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata
Verse 40 — Surah An-Najm 53:40
Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi
Verse 41 — Surah An-Najm 53:41
Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni
Verse 42 — Surah An-Najm 53:42
Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take
Verse 43 — Surah An-Najm 53:43
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka
Verse 44 — Surah An-Najm 53:44
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar
Verse 45 — Surah An-Najm 53:45
Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace
Verse 46 — Surah An-Najm 53:46
Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa
Verse 47 — Surah An-Najm 53:47
Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take
Verse 48 — Surah An-Najm 53:48
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar
Verse 49 — Surah An-Najm 53:49
Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira
Verse 50 — Surah An-Najm 53:50
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko
Verse 51 — Surah An-Najm 53:51
Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba
Verse 52 — Surah An-Najm 53:52
Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai
Verse 53 — Surah An-Najm 53:53
Da waɗanda aka birkice *ƙasarsu, Ya kãyar da su
Verse 54 — Surah An-Najm 53:54
Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su
Verse 55 — Surah An-Najm 53:55
To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake *yin shakka
Verse 56 — Surah An-Najm 53:56
wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko
Verse 57 — Surah An-Najm 53:57
Makusanciya* fa, tã yi kusa
Verse 58 — Surah An-Najm 53:58
Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta
Verse 59 — Surah An-Najm 53:59
Shin, kuma daga wannan *lãbãri kuke mãmãki
Verse 60 — Surah An-Najm 53:60
Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka
Verse 61 — Surah An-Najm 53:61
Alhãli kunã mãsu wãsã
Verse 62 — Surah An-Najm 53:62
To, ku yi tawãli'u *ga Allah, kuma ku bauta (masa)