Back to Languages

Hausa - Chapter 53 - An-Najm

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 32 — Surah An-Najm 53:32

Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa