Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 54 - Al-Qamar
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Qamar 54:1
Sã'a ta yi kusa, kuma wata *ya tsãge
Verse 2 — Surah Al-Qamar 54:2
Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa
Verse 3 — Surah Al-Qamar 54:3
Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi
Verse 4 — Surah Al-Qamar 54:4
Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu
Verse 5 — Surah Al-Qamar 54:5
Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni
Verse 6 — Surah Al-Qamar 54:6
Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama
Verse 7 — Surah Al-Qamar 54:7
¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse
Verse 8 — Surah Al-Qamar 54:8
Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya
Verse 9 — Surah Al-Qamar 54:9
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi
Verse 10 — Surah Al-Qamar 54:10
Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako
Verse 11 — Surah Al-Qamar 54:11
Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba
Verse 12 — Surah Al-Qamar 54:12
Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi
Verse 13 — Surah Al-Qamar 54:13
Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi
Verse 14 — Surah Al-Qamar 54:14
Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin
Verse 15 — Surah Al-Qamar 54:15
Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
Verse 16 — Surah Al-Qamar 54:16
To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na
Verse 17 — Surah Al-Qamar 54:17
Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
Verse 18 — Surah Al-Qamar 54:18
Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na
Verse 19 — Surah Al-Qamar 54:19
Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa
Verse 20 — Surah Al-Qamar 54:20
Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne
Verse 21 — Surah Al-Qamar 54:21
To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na
Verse 22 — Surah Al-Qamar 54:22
Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
Verse 23 — Surah Al-Qamar 54:23
Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin
Verse 24 — Surah Al-Qamar 54:24
Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã
Verse 25 — Surah Al-Qamar 54:25
Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai
Verse 26 — Surah Al-Qamar 54:26
Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan
Verse 27 — Surah Al-Qamar 54:27
Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar* ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri
Verse 28 — Surah Al-Qamar 54:28
Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa
Verse 29 — Surah Al-Qamar 54:29
Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta
Verse 30 — Surah Al-Qamar 54:30
To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na
Verse 31 — Surah Al-Qamar 54:31
Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge
Verse 32 — Surah Al-Qamar 54:32
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
Verse 33 — Surah Al-Qamar 54:33
Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi
Verse 34 — Surah Al-Qamar 54:34
Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba
Verse 35 — Surah Al-Qamar 54:35
Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde
Verse 36 — Surah Al-Qamar 54:36
Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin
Verse 37 — Surah Al-Qamar 54:37
Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na
Verse 38 — Surah Al-Qamar 54:38
Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe
Verse 39 — Surah Al-Qamar 54:39
To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na
Verse 40 — Surah Al-Qamar 54:40
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa
Verse 41 — Surah Al-Qamar 54:41
Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna
Verse 42 — Surah Al-Qamar 54:42
Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi
Verse 43 — Surah Al-Qamar 54:43
Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai
Verse 44 — Surah Al-Qamar 54:44
Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara
Verse 45 — Surah Al-Qamar 54:45
Zã a karya* tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu
Verse 46 — Surah Al-Qamar 54:46
Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci
Verse 47 — Surah Al-Qamar 54:47
Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka
Verse 48 — Surah Al-Qamar 54:48
Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar
Verse 49 — Surah Al-Qamar 54:49
Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri
Verse 50 — Surah Al-Qamar 54:50
Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido
Verse 51 — Surah Al-Qamar 54:51
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni
Verse 52 — Surah Al-Qamar 54:52
Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai
Verse 53 — Surah Al-Qamar 54:53
Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne
Verse 54 — Surah Al-Qamar 54:54
Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna
Verse 55 — Surah Al-Qamar 54:55
A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa