Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 55 - Ar-Rahman
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ar-Rahman 55:1
(Allah) Mai rahama
Verse 2 — Surah Ar-Rahman 55:2
Yã sanar da Alƙur'ani
Verse 3 — Surah Ar-Rahman 55:3
Yã halitta mutum
Verse 4 — Surah Ar-Rahman 55:4
Yã sanar da shi bayãni (magana)
Verse 5 — Surah Ar-Rahman 55:5
Rãnã da watã a kan lissãfi suke
Verse 6 — Surah Ar-Rahman 55:6
Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i
Verse 7 — Surah Ar-Rahman 55:7
Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli
Verse 8 — Surah Ar-Rahman 55:8
Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin
Verse 9 — Surah Ar-Rahman 55:9
Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin
Verse 10 — Surah Ar-Rahman 55:10
Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai
Verse 11 — Surah Ar-Rahman 55:11
A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa
Verse 12 — Surah Ar-Rahman 55:12
Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi
Verse 13 — Surah Ar-Rahman 55:13
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku *kuke ƙaryatãwa
Verse 14 — Surah Ar-Rahman 55:14
Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko
Verse 15 — Surah Ar-Rahman 55:15
Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã
Verse 16 — Surah Ar-Rahman 55:16
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 17 — Surah Ar-Rahman 55:17
Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã
Verse 18 — Surah Ar-Rahman 55:18
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 19 — Surah Ar-Rahman 55:19
Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa
Verse 20 — Surah Ar-Rahman 55:20
A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba
Verse 21 — Surah Ar-Rahman 55:21
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 22 — Surah Ar-Rahman 55:22
Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su
Verse 23 — Surah Ar-Rahman 55:23
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 24 — Surah Ar-Rahman 55:24
Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu
Verse 25 — Surah Ar-Rahman 55:25
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 26 — Surah Ar-Rahman 55:26
Dukkan wanda ke kanta* mai ƙãrẽwa ne
Verse 27 — Surah Ar-Rahman 55:27
Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa
Verse 28 — Surah Ar-Rahman 55:28
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 29 — Surah Ar-Rahman 55:29
wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani
Verse 30 — Surah Ar-Rahman 55:30
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 31 — Surah Ar-Rahman 55:31
Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ *mãsu nauyin halitta biyu
Verse 32 — Surah Ar-Rahman 55:32
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 33 — Surah Ar-Rahman 55:33
Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli
Verse 34 — Surah Ar-Rahman 55:34
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 35 — Surah Ar-Rahman 55:35
Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba
Verse 36 — Surah Ar-Rahman 55:36
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 37 — Surah Ar-Rahman 55:37
Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta
Verse 38 — Surah Ar-Rahman 55:38
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 39 — Surah Ar-Rahman 55:39
To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani
Verse 40 — Surah Ar-Rahman 55:40
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 41 — Surah Ar-Rahman 55:41
zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu
Verse 42 — Surah Ar-Rahman 55:42
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 43 — Surah Ar-Rahman 55:43
Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita
Verse 44 — Surah Ar-Rahman 55:44
Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa
Verse 45 — Surah Ar-Rahman 55:45
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 46 — Surah Ar-Rahman 55:46
Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu
Verse 47 — Surah Ar-Rahman 55:47
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 48 — Surah Ar-Rahman 55:48
Mãsu rassan itãce
Verse 49 — Surah Ar-Rahman 55:49
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 50 — Surah Ar-Rahman 55:50
A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna
Verse 51 — Surah Ar-Rahman 55:51
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 52 — Surah Ar-Rahman 55:52
A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari
Verse 53 — Surah Ar-Rahman 55:53
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 54 — Surah Ar-Rahman 55:54
Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke
Verse 55 — Surah Ar-Rahman 55:55
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 56 — Surah Ar-Rahman 55:56
A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani
Verse 57 — Surah Ar-Rahman 55:57
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 58 — Surah Ar-Rahman 55:58
Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni
Verse 59 — Surah Ar-Rahman 55:59
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 60 — Surah Ar-Rahman 55:60
Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa
Verse 61 — Surah Ar-Rahman 55:61
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 62 — Surah Ar-Rahman 55:62
Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu
Verse 63 — Surah Ar-Rahman 55:63
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 64 — Surah Ar-Rahman 55:64
Mãsu duhun inuwa
Verse 65 — Surah Ar-Rahman 55:65
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 66 — Surah Ar-Rahman 55:66
A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa
Verse 67 — Surah Ar-Rahman 55:67
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 68 — Surah Ar-Rahman 55:68
A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni
Verse 69 — Surah Ar-Rahman 55:69
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 70 — Surah Ar-Rahman 55:70
A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyawun hãlãye, mãsu kyaun halitta
Verse 71 — Surah Ar-Rahman 55:71
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 72 — Surah Ar-Rahman 55:72
Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi
Verse 73 — Surah Ar-Rahman 55:73
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 74 — Surah Ar-Rahman 55:74
Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani
Verse 75 — Surah Ar-Rahman 55:75
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 76 — Surah Ar-Rahman 55:76
Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa
Verse 77 — Surah Ar-Rahman 55:77
To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa
Verse 78 — Surah Ar-Rahman 55:78
Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka