Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 56 - Al-Waqiah
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Waqiah 56:1
Idan mai aukuwa ta auku
Verse 2 — Surah Al-Waqiah 56:2
Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta
Verse 3 — Surah Al-Waqiah 56:3
(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa
Verse 4 — Surah Al-Waqiah 56:4
Idan aka girgiza ƙasã girgizwa
Verse 5 — Surah Al-Waqiah 56:5
Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa
Verse 6 — Surah Al-Waqiah 56:6
Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa
Verse 7 — Surah Al-Waqiah 56:7
Kuma kun kasance nau'i uku
Verse 8 — Surah Al-Waqiah 56:8
Watau mazõwa dãma*. Mẽne ne mazõwa dãma
Verse 9 — Surah Al-Waqiah 56:9
Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu
Verse 10 — Surah Al-Waqiah 56:10
Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan
Verse 11 — Surah Al-Waqiah 56:11
Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar
Verse 12 — Surah Al-Waqiah 56:12
A ckin Aljannar ni'ima
Verse 13 — Surah Al-Waqiah 56:13
Jama'a ne daga mutãnen farko
Verse 14 — Surah Al-Waqiah 56:14
Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe
Verse 15 — Surah Al-Waqiah 56:15
(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu
Verse 16 — Surah Al-Waqiah 56:16
Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna
Verse 17 — Surah Al-Waqiah 56:17
Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu
Verse 18 — Surah Al-Waqiah 56:18
Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga
Verse 19 — Surah Al-Waqiah 56:19
Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa
Verse 20 — Surah Al-Waqiah 56:20
Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe
Verse 21 — Surah Al-Waqiah 56:21
Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa
Verse 22 — Surah Al-Waqiah 56:22
Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu
Verse 23 — Surah Al-Waqiah 56:23
Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye
Verse 24 — Surah Al-Waqiah 56:24
A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa
Verse 25 — Surah Al-Waqiah 56:25
Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi
Verse 26 — Surah Al-Waqiah 56:26
Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun
Verse 27 — Surah Al-Waqiah 56:27
Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma
Verse 28 — Surah Al-Waqiah 56:28
(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya
Verse 29 — Surah Al-Waqiah 56:29
Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya
Verse 30 — Surah Al-Waqiah 56:30
Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya
Verse 31 — Surah Al-Waqiah 56:31
Da wani ruwa mai gudãna
Verse 32 — Surah Al-Waqiah 56:32
Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa
Verse 33 — Surah Al-Waqiah 56:33
Bã su yankẽwa kuma bã a hana su
Verse 34 — Surah Al-Waqiah 56:34
Da wasu shimfiɗu maɗaukaka
Verse 35 — Surah Al-Waqiah 56:35
Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa
Verse 36 — Surah Al-Waqiah 56:36
Sa'an nan Muka sanya su budurwai
Verse 37 — Surah Al-Waqiah 56:37
Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya
Verse 38 — Surah Al-Waqiah 56:38
Ga mazõwa dãma
Verse 39 — Surah Al-Waqiah 56:39
Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko
Verse 40 — Surah Al-Waqiah 56:40
Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe
Verse 41 — Surah Al-Waqiah 56:41
Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu
Verse 42 — Surah Al-Waqiah 56:42
Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi
Verse 43 — Surah Al-Waqiah 56:43
Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi
Verse 44 — Surah Al-Waqiah 56:44
Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba
Verse 45 — Surah Al-Waqiah 56:45
Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi
Verse 46 — Surah Al-Waqiah 56:46
Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma
Verse 47 — Surah Al-Waqiah 56:47
Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan
Verse 48 — Surah Al-Waqiah 56:48
Shin, kuma da ubanninmu na farko
Verse 49 — Surah Al-Waqiah 56:49
Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe
Verse 50 — Surah Al-Waqiah 56:50
Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne
Verse 51 — Surah Al-Waqiah 56:51
Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa
Verse 52 — Surah Al-Waqiah 56:52
Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)
Verse 53 — Surah Al-Waqiah 56:53
Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta
Verse 54 — Surah Al-Waqiah 56:54
Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi
Verse 55 — Surah Al-Waqiah 56:55
Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa
Verse 56 — Surah Al-Waqiah 56:56
Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako
Verse 57 — Surah Al-Waqiah 56:57
Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba
Verse 58 — Surah Al-Waqiah 56:58
Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi
Verse 59 — Surah Al-Waqiah 56:59
Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa
Verse 60 — Surah Al-Waqiah 56:60
Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa* ba
Verse 61 — Surah Al-Waqiah 56:61
A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba
Verse 62 — Surah Al-Waqiah 56:62
Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba
Verse 63 — Surah Al-Waqiah 56:63
Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa
Verse 64 — Surah Al-Waqiah 56:64
Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa
Verse 65 — Surah Al-Waqiah 56:65
Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki
Verse 66 — Surah Al-Waqiah 56:66
(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra
Verse 67 — Surah Al-Waqiah 56:67
Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa
Verse 68 — Surah Al-Waqiah 56:68
Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha
Verse 69 — Surah Al-Waqiah 56:69
Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa
Verse 70 — Surah Al-Waqiah 56:70
Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa
Verse 71 — Surah Al-Waqiah 56:71
Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa
Verse 72 — Surah Al-Waqiah 56:72
Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa
Verse 73 — Surah Al-Waqiah 56:73
Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji
Verse 74 — Surah Al-Waqiah 56:74
Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma
Verse 75 — Surah Al-Waqiah 56:75
To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri
Verse 76 — Surah Al-Waqiah 56:76
Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani
Verse 77 — Surah Al-Waqiah 56:77
Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja
Verse 78 — Surah Al-Waqiah 56:78
A cikin wani littafi tsararre
Verse 79 — Surah Al-Waqiah 56:79
Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake
Verse 80 — Surah Al-Waqiah 56:80
Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta
Verse 81 — Surah Al-Waqiah 56:81
Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa
Verse 82 — Surah Al-Waqiah 56:82
Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)
Verse 83 — Surah Al-Waqiah 56:83
To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa)
Verse 84 — Surah Al-Waqiah 56:84
Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo
Verse 85 — Surah Al-Waqiah 56:85
Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani
Verse 86 — Surah Al-Waqiah 56:86
To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba
Verse 87 — Surah Al-Waqiah 56:87
Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya
Verse 88 — Surah Al-Waqiah 56:88
To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta
Verse 89 — Surah Al-Waqiah 56:89
Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima
Verse 90 — Surah Al-Waqiah 56:90
Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma
Verse 91 — Surah Al-Waqiah 56:91
Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma
Verse 92 — Surah Al-Waqiah 56:92
Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun
Verse 93 — Surah Al-Waqiah 56:93
Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi
Verse 94 — Surah Al-Waqiah 56:94
Da ƙõnuwa da Jahĩm
Verse 95 — Surah Al-Waqiah 56:95
Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni
Verse 96 — Surah Al-Waqiah 56:96
Sabõda haka, ka tsarkake* sũnan Ubangijinka, Mai karimci