Back to Languages

Hausa - Chapter 53 - An-Najm

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 23 — Surah An-Najm 53:23

Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar* ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton)