Back to Languages

Hausa - Chapter 65 - At-Talaq

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 11 — Surah At-Talaq 65:11

Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata* masa arziki