Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 72 - Al-Jinn
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Jinn 72:1
Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki
Verse 2 — Surah Al-Jinn 72:2
Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba
Verse 3 — Surah Al-Jinn 72:3
Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba
Verse 4 — Surah Al-Jinn 72:4
Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah
Verse 5 — Surah Al-Jinn 72:5
Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah
Verse 6 — Surah Al-Jinn 72:6
Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai
Verse 7 — Surah Al-Jinn 72:7
Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba
Verse 8 — Surah Al-Jinn 72:8
Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye
Verse 9 — Surah Al-Jinn 72:9
Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa
Verse 10 — Surah Al-Jinn 72:10
Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne
Verse 11 — Surah Al-Jinn 72:11
Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam
Verse 12 — Surah Al-Jinn 72:12
Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba
Verse 13 — Surah Al-Jinn 72:13
Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba
Verse 14 — Surah Al-Jinn 72:14
Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa
Verse 15 — Surah Al-Jinn 72:15
Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama
Verse 16 — Surah Al-Jinn 72:16
Kuma dã sun tsayu* sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa
Verse 17 — Surah Al-Jinn 72:17
Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa
Verse 18 — Surah Al-Jinn 72:18
Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)
Verse 19 — Surah Al-Jinn 72:19
Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah* ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa
Verse 20 — Surah Al-Jinn 72:20
Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba
Verse 21 — Surah Al-Jinn 72:21
Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri
Verse 22 — Surah Al-Jinn 72:22
Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi
Verse 23 — Surah Al-Jinn 72:23
Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da Manzon Sa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada
Verse 24 — Surah Al-Jinn 72:24
Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi
Verse 25 — Surah Al-Jinn 72:25
Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya masa dõgon ajali
Verse 26 — Surah Al-Jinn 72:26
Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinsa ga kowa
Verse 27 — Surah Al-Jinn 72:27
Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya* gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi
Verse 28 — Surah Al-Jinn 72:28
Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga