Back to Languages

Hausa - Chapter 73 - Al-Muzzammil

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Muzzammil 73:1

Yã wanda ya lulluɓe

Verse 2 — Surah Al-Muzzammil 73:2

Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan

Verse 3 — Surah Al-Muzzammil 73:3

Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi

Verse 4 — Surah Al-Muzzammil 73:4

Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki

Verse 5 — Surah Al-Muzzammil 73:5

Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi

Verse 6 — Surah Al-Muzzammil 73:6

Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana

Verse 7 — Surah Al-Muzzammil 73:7

Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo

Verse 8 — Surah Al-Muzzammil 73:8

Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa

Verse 9 — Surah Al-Muzzammil 73:9

Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili

Verse 10 — Surah Al-Muzzammil 73:10

Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo

Verse 11 — Surah Al-Muzzammil 73:11

Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan

Verse 12 — Surah Al-Muzzammil 73:12

Lalle ne, a wurin Mu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm

Verse 13 — Surah Al-Muzzammil 73:13

Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi

Verse 14 — Surah Al-Muzzammil 73:14

Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã

Verse 15 — Surah Al-Muzzammil 73:15

Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo* mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo** zuwaga Fir'auna

Verse 16 — Surah Al-Muzzammil 73:16

Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani

Verse 17 — Surah Al-Muzzammil 73:17

To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura

Verse 18 — Surah Al-Muzzammil 73:18

Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa

Verse 19 — Surah Al-Muzzammil 73:19

Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa

Verse 20 — Surah Al-Muzzammil 73:20

Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai