Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 74 - Al-Muddaththir
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Muddaththir 74:1
Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi
Verse 2 — Surah Al-Muddaththir 74:2
Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
Verse 3 — Surah Al-Muddaththir 74:3
Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi
Verse 4 — Surah Al-Muddaththir 74:4
Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su
Verse 5 — Surah Al-Muddaththir 74:5
Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu
Verse 6 — Surah Al-Muddaththir 74:6
Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
Verse 7 — Surah Al-Muddaththir 74:7
Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
Verse 8 — Surah Al-Muddaththir 74:8
To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho
Verse 9 — Surah Al-Muddaththir 74:9
To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
Verse 10 — Surah Al-Muddaththir 74:10
A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne
Verse 11 — Surah Al-Muddaththir 74:11
Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai
Verse 12 — Surah Al-Muddaththir 74:12
Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
Verse 13 — Surah Al-Muddaththir 74:13
Da ɗiyã halartattu
Verse 14 — Surah Al-Muddaththir 74:14
Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa
Verse 15 — Surah Al-Muddaththir 74:15
Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri
Verse 16 — Surah Al-Muddaththir 74:16
Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyin Mu, mai tsaurin kai
Verse 17 — Surah Al-Muddaththir 74:17
Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa
Verse 18 — Surah Al-Muddaththir 74:18
Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)
Verse 19 — Surah Al-Muddaththir 74:19
Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara
Verse 20 — Surah Al-Muddaththir 74:20
Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara
Verse 21 — Surah Al-Muddaththir 74:21
Sa'an nan, ya yi tunãni
Verse 22 — Surah Al-Muddaththir 74:22
Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk
Verse 23 — Surah Al-Muddaththir 74:23
Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa
Verse 24 — Surah Al-Muddaththir 74:24
Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito
Verse 25 — Surah Al-Muddaththir 74:25
Wannan maganar mutum dai ce
Verse 26 — Surah Al-Muddaththir 74:26
Zã Ni ƙõna shi da Saƙar
Verse 27 — Surah Al-Muddaththir 74:27
Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar
Verse 28 — Surah Al-Muddaththir 74:28
Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari
Verse 29 — Surah Al-Muddaththir 74:29
Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna)
Verse 30 — Surah Al-Muddaththir 74:30
A kanta akwai (matsara) gõma shã tara
Verse 31 — Surah Al-Muddaththir 74:31
Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum
Verse 32 — Surah Al-Muddaththir 74:32
A'aha! Ina rantsuwa da watã
Verse 33 — Surah Al-Muddaththir 74:33
Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya
Verse 34 — Surah Al-Muddaththir 74:34
Da sãfiya idan ta wãye
Verse 35 — Surah Al-Muddaththir 74:35
Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce
Verse 36 — Surah Al-Muddaththir 74:36
Mai gargaɗĩ ce ga mutum
Verse 37 — Surah Al-Muddaththir 74:37
Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta
Verse 38 — Surah Al-Muddaththir 74:38
Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce
Verse 39 — Surah Al-Muddaththir 74:39
Fãce mutãnen dãma
Verse 40 — Surah Al-Muddaththir 74:40
A cikin Aljanna suna tambayar jũna
Verse 41 — Surah Al-Muddaththir 74:41
Game da mãsu laifi
Verse 42 — Surah Al-Muddaththir 74:42
(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar
Verse 43 — Surah Al-Muddaththir 74:43
Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba
Verse 44 — Surah Al-Muddaththir 74:44
Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba
Verse 45 — Surah Al-Muddaththir 74:45
Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa
Verse 46 — Surah Al-Muddaththir 74:46
Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako
Verse 47 — Surah Al-Muddaththir 74:47
Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana
Verse 48 — Surah Al-Muddaththir 74:48
Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba
Verse 49 — Surah Al-Muddaththir 74:49
Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya
Verse 50 — Surah Al-Muddaththir 74:50
Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne
Verse 51 — Surah Al-Muddaththir 74:51
Sun gudu daga zãki
Verse 52 — Surah Al-Muddaththir 74:52
A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
Verse 53 — Surah Al-Muddaththir 74:53
A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira
Verse 54 — Surah Al-Muddaththir 74:54
A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce
Verse 55 — Surah Al-Muddaththir 74:55
Dõmin wanda ya so, ya tuna
Verse 56 — Surah Al-Muddaththir 74:56
Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara