Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 75 - Al-Qiyamah
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Qiyamah 75:1
Bã sai Nã yi rantsuwa* da Rãnar ¡iyãma ba
Verse 2 — Surah Al-Qiyamah 75:2
Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba
Verse 3 — Surah Al-Qiyamah 75:3
Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba
Verse 4 — Surah Al-Qiyamah 75:4
Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa
Verse 5 — Surah Al-Qiyamah 75:5
Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa
Verse 6 — Surah Al-Qiyamah 75:6
Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma
Verse 7 — Surah Al-Qiyamah 75:7
To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli)
Verse 8 — Surah Al-Qiyamah 75:8
Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe)
Verse 9 — Surah Al-Qiyamah 75:9
Aka tãra rãnã da watã
Verse 10 — Surah Al-Qiyamah 75:10
Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu
Verse 11 — Surah Al-Qiyamah 75:11
A'aha! bãbu mafaka
Verse 12 — Surah Al-Qiyamah 75:12
zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake
Verse 13 — Surah Al-Qiyamah 75:13
Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar
Verse 14 — Surah Al-Qiyamah 75:14
Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne
Verse 15 — Surah Al-Qiyamah 75:15
Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba)
Verse 16 — Surah Al-Qiyamah 75:16
Kada ka mõtsar* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni)
Verse 17 — Surah Al-Qiyamah 75:17
Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa
Verse 18 — Surah Al-Qiyamah 75:18
To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa
Verse 19 — Surah Al-Qiyamah 75:19
sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa
Verse 20 — Surah Al-Qiyamah 75:20
A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne
Verse 21 — Surah Al-Qiyamah 75:21
Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira)
Verse 22 — Surah Al-Qiyamah 75:22
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne
Verse 23 — Surah Al-Qiyamah 75:23
Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne
Verse 24 — Surah Al-Qiyamah 75:24
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne
Verse 25 — Surah Al-Qiyamah 75:25
Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso
Verse 26 — Surah Al-Qiyamah 75:26
A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai
Verse 27 — Surah Al-Qiyamah 75:27
kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada
Verse 28 — Surah Al-Qiyamah 75:28
Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce
Verse 29 — Surah Al-Qiyamah 75:29
Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri
Verse 30 — Surah Al-Qiyamah 75:30
Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa* take
Verse 31 — Surah Al-Qiyamah 75:31
To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba
Verse 32 — Surah Al-Qiyamah 75:32
Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya
Verse 33 — Surah Al-Qiyamah 75:33
Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama
Verse 34 — Surah Al-Qiyamah 75:34
Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa
Verse 35 — Surah Al-Qiyamah 75:35
Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa
Verse 36 — Surah Al-Qiyamah 75:36
Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)
Verse 37 — Surah Al-Qiyamah 75:37
Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
Verse 38 — Surah Al-Qiyamah 75:38
Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa
Verse 39 — Surah Al-Qiyamah 75:39
Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace
Verse 40 — Surah Al-Qiyamah 75:40
Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu