Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 76 - Al-Insan
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Insan 76:1
Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata
Verse 2 — Surah Al-Insan 76:2
Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani
Verse 3 — Surah Al-Insan 76:3
Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci
Verse 4 — Surah Al-Insan 76:4
Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr
Verse 5 — Surah Al-Insan 76:5
Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne
Verse 6 — Surah Al-Insan 76:6
Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa
Verse 7 — Surah Al-Insan 76:7
Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne
Verse 8 — Surah Al-Insan 76:8
Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme
Verse 9 — Surah Al-Insan 76:9
(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya
Verse 10 — Surah Al-Insan 76:10
Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa
Verse 11 — Surah Al-Insan 76:11
Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki
Verse 12 — Surah Al-Insan 76:12
Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini
Verse 13 — Surah Al-Insan 76:13
Sunã mãsu zaman ginciri,* a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura
Verse 14 — Surah Al-Insan 76:14
Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa
Verse 15 — Surah Al-Insan 76:15
Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau
Verse 16 — Surah Al-Insan 76:16
¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta
Verse 17 — Surah Al-Insan 76:17
Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne
Verse 18 — Surah Al-Insan 76:18
Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil
Verse 19 — Surah Al-Insan 76:19
Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa
Verse 20 — Surah Al-Insan 76:20
Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba
Verse 21 — Surah Al-Insan 76:21
Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki)
Verse 22 — Surah Al-Insan 76:22
(A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa
Verse 23 — Surah Al-Insan 76:23
Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa
Verse 24 — Surah Al-Insan 76:24
Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci
Verse 25 — Surah Al-Insan 76:25
Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice
Verse 26 — Surah Al-Insan 76:26
Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo
Verse 27 — Surah Al-Insan 76:27
Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi
Verse 28 — Surah Al-Insan 76:28
Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa
Verse 29 — Surah Al-Insan 76:29
Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa
Verse 30 — Surah Al-Insan 76:30
Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima
Verse 31 — Surah Al-Insan 76:31
Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi