Back to Languages

Hausa - Chapter 77 - Al-Mursalat

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Mursalat 77:1

Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna

Verse 2 — Surah Al-Mursalat 77:2

Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi

Verse 3 — Surah Al-Mursalat 77:3

Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa

Verse 4 — Surah Al-Mursalat 77:4

sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa

Verse 5 — Surah Al-Mursalat 77:5

Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni

Verse 6 — Surah Al-Mursalat 77:6

Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi

Verse 7 — Surah Al-Mursalat 77:7

Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne

Verse 8 — Surah Al-Mursalat 77:8

To, idan taurãri aka shãfe haskensu

Verse 9 — Surah Al-Mursalat 77:9

Kuma, idan sama aka tsãge ta

Verse 10 — Surah Al-Mursalat 77:10

Kuma, idan duwãtsu aka nike su

Verse 11 — Surah Al-Mursalat 77:11

Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su

Verse 12 — Surah Al-Mursalat 77:12

Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali

Verse 13 — Surah Al-Mursalat 77:13

Domin rãnar rarrabẽwa

Verse 14 — Surah Al-Mursalat 77:14

Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa

Verse 15 — Surah Al-Mursalat 77:15

Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 16 — Surah Al-Mursalat 77:16

Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba

Verse 17 — Surah Al-Mursalat 77:17

Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe

Verse 18 — Surah Al-Mursalat 77:18

Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi

Verse 19 — Surah Al-Mursalat 77:19

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 20 — Surah Al-Mursalat 77:20

Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba

Verse 21 — Surah Al-Mursalat 77:21

Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce

Verse 22 — Surah Al-Mursalat 77:22

Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna

Verse 23 — Surah Al-Mursalat 77:23

Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa

Verse 24 — Surah Al-Mursalat 77:24

Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 25 — Surah Al-Mursalat 77:25

Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba

Verse 26 — Surah Al-Mursalat 77:26

Ga rãyayyu da matattu

Verse 27 — Surah Al-Mursalat 77:27

Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi

Verse 28 — Surah Al-Mursalat 77:28

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 29 — Surah Al-Mursalat 77:29

Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi

Verse 30 — Surah Al-Mursalat 77:30

Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku

Verse 31 — Surah Al-Mursalat 77:31

Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta

Verse 32 — Surah Al-Mursalat 77:32

Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye

Verse 33 — Surah Al-Mursalat 77:33

Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe

Verse 34 — Surah Al-Mursalat 77:34

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 35 — Surah Al-Mursalat 77:35

Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba

Verse 36 — Surah Al-Mursalat 77:36

Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari

Verse 37 — Surah Al-Mursalat 77:37

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 38 — Surah Al-Mursalat 77:38

Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko

Verse 39 — Surah Al-Mursalat 77:39

To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita

Verse 40 — Surah Al-Mursalat 77:40

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 41 — Surah Al-Mursalat 77:41

Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari

Verse 42 — Surah Al-Mursalat 77:42

Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari

Verse 43 — Surah Al-Mursalat 77:43

(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa

Verse 44 — Surah Al-Mursalat 77:44

Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

Verse 45 — Surah Al-Mursalat 77:45

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 46 — Surah Al-Mursalat 77:46

(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne

Verse 47 — Surah Al-Mursalat 77:47

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 48 — Surah Al-Mursalat 77:48

Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba

Verse 49 — Surah Al-Mursalat 77:49

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 50 — Surah Al-Mursalat 77:50

To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni