Back to Languages

Hausa - Chapter 78 - An-Naba

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah An-Naba 78:1

A kan mẽ suke tambayar jũna

Verse 2 — Surah An-Naba 78:2

A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)

Verse 3 — Surah An-Naba 78:3

Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa

Verse 4 — Surah An-Naba 78:4

Verse 5 — Surah An-Naba 78:5

Kuma, a'aha! Zã su sani

Verse 6 — Surah An-Naba 78:6

Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba

Verse 7 — Surah An-Naba 78:7

Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)

Verse 8 — Surah An-Naba 78:8

Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã

Verse 9 — Surah An-Naba 78:9

Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa

Verse 10 — Surah An-Naba 78:10

Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura

Verse 11 — Surah An-Naba 78:11

Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci

Verse 12 — Surah An-Naba 78:12

Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi

Verse 13 — Surah An-Naba 78:13

Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)

Verse 14 — Surah An-Naba 78:14

Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba

Verse 15 — Surah An-Naba 78:15

Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi

Verse 16 — Surah An-Naba 78:16

Da itãcen lambuna mãsu lillibniya

Verse 17 — Surah An-Naba 78:17

Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci

Verse 18 — Surah An-Naba 78:18

Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a

Verse 19 — Surah An-Naba 78:19

Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi

Verse 20 — Surah An-Naba 78:20

Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra

Verse 21 — Surah An-Naba 78:21

Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata

Verse 22 — Surah An-Naba 78:22

Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma

Verse 23 — Surah An-Naba 78:23

Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna

Verse 24 — Surah An-Naba 78:24

Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha

Verse 25 — Surah An-Naba 78:25

Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini

Verse 26 — Surah An-Naba 78:26

Sakamako mai dãcẽwa

Verse 27 — Surah An-Naba 78:27

Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi

Verse 28 — Surah An-Naba 78:28

Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa

Verse 29 — Surah An-Naba 78:29

Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce

Verse 30 — Surah An-Naba 78:30

Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba

Verse 31 — Surah An-Naba 78:31

Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo

Verse 32 — Surah An-Naba 78:32

Verse 33 — Surah An-Naba 78:33

Da yan Mata tsaraikun Juna

Verse 34 — Surah An-Naba 78:34

Da hinjãlan giya cikakku

Verse 35 — Surah An-Naba 78:35

Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa

Verse 36 — Surah An-Naba 78:36

Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa

Verse 37 — Surah An-Naba 78:37

Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi

Verse 38 — Surah An-Naba 78:38

Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai

Verse 39 — Surah An-Naba 78:39

Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa

Verse 40 — Surah An-Naba 78:40

Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya