Back to Languages

Hausa - Chapter 71 - Nuh

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Nuh 71:1

Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu

Verse 2 — Surah Nuh 71:2

Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa

Verse 3 — Surah Nuh 71:3

Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõron Sa, kuma ku bĩ ni

Verse 4 — Surah Nuh 71:4

Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)

Verse 5 — Surah Nuh 71:5

(Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini

Verse 6 — Surah Nuh 71:6

To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)

Verse 7 — Surah Nuh 71:7

Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai

Verse 8 — Surah Nuh 71:8

Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane

Verse 9 — Surah Nuh 71:9

Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri

Verse 10 — Surah Nuh 71:10

Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne

Verse 11 — Surah Nuh 71:11

Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga

Verse 12 — Surah Nuh 71:12

Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna

Verse 13 — Surah Nuh 71:13

Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah

Verse 14 — Surah Nuh 71:14

Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye

Verse 15 — Surah Nuh 71:15

Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba

Verse 16 — Surah Nuh 71:16

Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila

Verse 17 — Surah Nuh 71:17

Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa

Verse 18 — Surah Nuh 71:18

Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa

Verse 19 — Surah Nuh 71:19

Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya

Verse 20 — Surah Nuh 71:20

Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi

Verse 21 — Surah Nuh 71:21

Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra

Verse 22 — Surah Nuh 71:22

Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba

Verse 23 — Surah Nuh 71:23

Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Yans uƙa da Nasra

Verse 24 — Surah Nuh 71:24

Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata

Verse 25 — Surah Nuh 71:25

Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba

Verse 26 — Surah Nuh 71:26

Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida

Verse 27 — Surah Nuh 71:27

Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyin Ka, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci

Verse 28 — Surah Nuh 71:28

Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka