Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 70 - Al-Maarij
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Maarij 70:1
Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa
Verse 2 — Surah Al-Maarij 70:2
Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa
Verse 3 — Surah Al-Maarij 70:3
Daga Allah Mai matãkala
Verse 4 — Surah Al-Maarij 70:4
Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne
Verse 5 — Surah Al-Maarij 70:5
Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo
Verse 6 — Surah Al-Maarij 70:6
Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa
Verse 7 — Surah Al-Maarij 70:7
Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa
Verse 8 — Surah Al-Maarij 70:8
Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa
Verse 9 — Surah Al-Maarij 70:9
Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi
Verse 10 — Surah Al-Maarij 70:10
Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake
Verse 11 — Surah Al-Maarij 70:11
Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa
Verse 12 — Surah Al-Maarij 70:12
Da matarsa da ɗan'uwansa
Verse 13 — Surah Al-Maarij 70:13
Da danginsa, mãsu tattarã shi
Verse 14 — Surah Al-Maarij 70:14
Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi
Verse 15 — Surah Al-Maarij 70:15
A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã
Verse 16 — Surah Al-Maarij 70:16
Mai twãle fãtar goshi
Verse 17 — Surah Al-Maarij 70:17
Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai
Verse 18 — Surah Al-Maarij 70:18
Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka
Verse 19 — Surah Al-Maarij 70:19
Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi
Verse 20 — Surah Al-Maarij 70:20
Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri
Verse 21 — Surah Al-Maarij 70:21
Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa
Verse 22 — Surah Al-Maarij 70:22
Sai mãsu yin salla
Verse 23 — Surah Al-Maarij 70:23
Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne
Verse 24 — Surah Al-Maarij 70:24
Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne
Verse 25 — Surah Al-Maarij 70:25
Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon
Verse 26 — Surah Al-Maarij 70:26
Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako
Verse 27 — Surah Al-Maarij 70:27
Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro
Verse 28 — Surah Al-Maarij 70:28
Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce
Verse 29 — Surah Al-Maarij 70:29
Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne
Verse 30 — Surah Al-Maarij 70:30
Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne
Verse 31 — Surah Al-Maarij 70:31
To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka
Verse 32 — Surah Al-Maarij 70:32
Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne
Verse 33 — Surah Al-Maarij 70:33
Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne
Verse 34 — Surah Al-Maarij 70:34
Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne
Verse 35 — Surah Al-Maarij 70:35
Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
Verse 36 — Surah Al-Maarij 70:36
Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu)
Verse 37 — Surah Al-Maarij 70:37
Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a
Verse 38 — Surah Al-Maarij 70:38
Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)
Verse 39 — Surah Al-Maarij 70:39
A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani
Verse 40 — Surah Al-Maarij 70:40
Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne
Verse 41 — Surah Al-Maarij 70:41
Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba
Verse 42 — Surah Al-Maarij 70:42
Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita)
Verse 43 — Surah Al-Maarij 70:43
Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa
Verse 44 — Surah Al-Maarij 70:44
Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa)