Back to Languages

Hausa - Chapter 69 - Al-Haqqah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Haqqah 69:1

Verse 2 — Surah Al-Haqqah 69:2

Mẽne ne kiran gaskiya

Verse 3 — Surah Al-Haqqah 69:3

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya

Verse 4 — Surah Al-Haqqah 69:4

Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya

Verse 5 — Surah Al-Haqqah 69:5

To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani

Verse 6 — Surah Al-Haqqah 69:6

Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi

Verse 7 — Surah Al-Haqqah 69:7

(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi

Verse 8 — Surah Al-Haqqah 69:8

To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu

Verse 9 — Surah Al-Haqqah 69:9

Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi

Verse 10 — Surah Al-Haqqah 69:10

Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani)

Verse 11 — Surah Al-Haqqah 69:11

Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan

Verse 12 — Surah Al-Haqqah 69:12

Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi)

Verse 13 — Surah Al-Haqqah 69:13

To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya

Verse 14 — Surah Al-Haqqah 69:14

Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya

Verse 15 — Surah Al-Haqqah 69:15

A ran nan, mai aukuwa zã ta auku

Verse 16 — Surah Al-Haqqah 69:16

Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce

Verse 17 — Surah Al-Haqqah 69:17

Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar

Verse 18 — Surah Al-Haqqah 69:18

A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa

Verse 19 — Surah Al-Haqqah 69:19

To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina

Verse 20 — Surah Al-Haqqah 69:20

Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne

Verse 21 — Surah Al-Haqqah 69:21

Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda

Verse 22 — Surah Al-Haqqah 69:22

A cikin Aljanna maɗaukakiya

Verse 23 — Surah Al-Haqqah 69:23

Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba)

Verse 24 — Surah Al-Haqqah 69:24

(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige

Verse 25 — Surah Al-Haqqah 69:25

Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba

Verse 26 — Surah Al-Haqqah 69:26

Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba

Verse 27 — Surah Al-Haqqah 69:27

In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce

Verse 28 — Surah Al-Haqqah 69:28

Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba

Verse 29 — Surah Al-Haqqah 69:29

Ĩkona ya ɓace mini

Verse 30 — Surah Al-Haqqah 69:30

(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi

Verse 31 — Surah Al-Haqqah 69:31

Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi

Verse 32 — Surah Al-Haqqah 69:32

Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi

Verse 33 — Surah Al-Haqqah 69:33

Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma

Verse 34 — Surah Al-Haqqah 69:34

Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci

Verse 35 — Surah Al-Haqqah 69:35

Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi

Verse 36 — Surah Al-Haqqah 69:36

Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn

Verse 37 — Surah Al-Haqqah 69:37

Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci

Verse 38 — Surah Al-Haqqah 69:38

To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba

Verse 39 — Surah Al-Haqqah 69:39

Da abin da bã ku iya gani

Verse 40 — Surah Al-Haqqah 69:40

Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne

Verse 41 — Surah Al-Haqqah 69:41

Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata

Verse 42 — Surah Al-Haqqah 69:42

Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa

Verse 43 — Surah Al-Haqqah 69:43

Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka

Verse 44 — Surah Al-Haqqah 69:44

Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu

Verse 45 — Surah Al-Haqqah 69:45

Dã Mun kãma shi da dãma

Verse 46 — Surah Al-Haqqah 69:46

sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã

Verse 47 — Surah Al-Haqqah 69:47

Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbar Mu) daga gare shi

Verse 48 — Surah Al-Haqqah 69:48

Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa

Verse 49 — Surah Al-Haqqah 69:49

Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa

Verse 50 — Surah Al-Haqqah 69:50

Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai

Verse 51 — Surah Al-Haqqah 69:51

Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini

Verse 52 — Surah Al-Haqqah 69:52

Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma