Back to Languages

Hausa - Chapter 68 - Al-Qalam

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Qalam 68:1

Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa

Verse 2 — Surah Al-Qalam 68:2

Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba

Verse 3 — Surah Al-Qalam 68:3

Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa

Verse 4 — Surah Al-Qalam 68:4

Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya

Verse 5 — Surah Al-Qalam 68:5

Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani

Verse 6 — Surah Al-Qalam 68:6

Ga wanenku haukã take

Verse 7 — Surah Al-Qalam 68:7

Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkin Sa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa

Verse 8 — Surah Al-Qalam 68:8

Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa

Verse 9 — Surah Al-Qalam 68:9

Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta

Verse 10 — Surah Al-Qalam 68:10

Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce

Verse 11 — Surah Al-Qalam 68:11

Mai zunɗe, mai yãwo da gulma

Verse 12 — Surah Al-Qalam 68:12

Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi

Verse 13 — Surah Al-Qalam 68:13

Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri)

Verse 14 — Surah Al-Qalam 68:14

Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya

Verse 15 — Surah Al-Qalam 68:15

Idan ana karanta masa ãyõyin Mu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne

Verse 16 — Surah Al-Qalam 68:16

Zã Mu yi masa alãma a kan hanci

Verse 17 — Surah Al-Qalam 68:17

Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci

Verse 18 — Surah Al-Qalam 68:18

Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa

Verse 19 — Surah Al-Qalam 68:19

Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci

Verse 20 — Surah Al-Qalam 68:20

Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare

Verse 21 — Surah Al-Qalam 68:21

Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci

Verse 22 — Surah Al-Qalam 68:22

Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa

Verse 23 — Surah Al-Qalam 68:23

Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa)

Verse 24 — Surah Al-Qalam 68:24

Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau

Verse 25 — Surah Al-Qalam 68:25

Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu

Verse 26 — Surah Al-Qalam 68:26

Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)

Verse 27 — Surah Al-Qalam 68:27

Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne

Verse 28 — Surah Al-Qalam 68:28

Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah

Verse 29 — Surah Al-Qalam 68:29

Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai

Verse 30 — Surah Al-Qalam 68:30

Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu

Verse 31 — Surah Al-Qalam 68:31

Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka

Verse 32 — Surah Al-Qalam 68:32

Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne

Verse 33 — Surah Al-Qalam 68:33

Haka dai azãbar* take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã

Verse 34 — Surah Al-Qalam 68:34

Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima

Verse 35 — Surah Al-Qalam 68:35

Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi

Verse 36 — Surah Al-Qalam 68:36

Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)

Verse 37 — Surah Al-Qalam 68:37

Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa

Verse 38 — Surah Al-Qalam 68:38

Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa

Verse 39 — Surah Al-Qalam 68:39

Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku

Verse 40 — Surah Al-Qalam 68:40

Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)

Verse 41 — Surah Al-Qalam 68:41

Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya

Verse 42 — Surah Al-Qalam 68:42

Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai bã zã su iyãwa ba

Verse 43 — Surah Al-Qalam 68:43

Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi)

Verse 44 — Surah Al-Qalam 68:44

Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba

Verse 45 — Surah Al-Qalam 68:45

Ina jinkirtã musu, lalle kaidi Na mai ƙarfi ne

Verse 46 — Surah Al-Qalam 68:46

Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu

Verse 47 — Surah Al-Qalam 68:47

Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne

Verse 48 — Surah Al-Qalam 68:48

Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi

Verse 49 — Surah Al-Qalam 68:49

Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi

Verse 50 — Surah Al-Qalam 68:50

Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki

Verse 51 — Surah Al-Qalam 68:51

Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne

Verse 52 — Surah Al-Qalam 68:52

Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya