Back to Languages

Hausa - Chapter 80 - Abasa

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Abasa 80:1

Yã game huska* kuma ya jũya bãya

Verse 2 — Surah Abasa 80:2

Sabõda makãho yã je masa

Verse 3 — Surah Abasa 80:3

To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka

Verse 4 — Surah Abasa 80:4

Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi

Verse 5 — Surah Abasa 80:5

Amma wanda ya wadãtu da dũkiya

Verse 6 — Surah Abasa 80:6

Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi

Verse 7 — Surah Abasa 80:7

To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba

Verse 8 — Surah Abasa 80:8

Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa

Verse 9 — Surah Abasa 80:9

Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah

Verse 10 — Surah Abasa 80:10

Kai kuma kã shagala ga barinsa

Verse 11 — Surah Abasa 80:11

A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce

Verse 12 — Surah Abasa 80:12

Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah)

Verse 13 — Surah Abasa 80:13

(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa

Verse 14 — Surah Abasa 80:14

Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa

Verse 15 — Surah Abasa 80:15

A cikin hannãyen mala'iku marubũta

Verse 16 — Surah Abasa 80:16

Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah

Verse 17 — Surah Abasa 80:17

An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa

Verse 18 — Surah Abasa 80:18

Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi

Verse 19 — Surah Abasa 80:19

Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye)

Verse 20 — Surah Abasa 80:20

Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa

Verse 21 — Surah Abasa 80:21

Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari

Verse 22 — Surah Abasa 80:22

Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi

Verse 23 — Surah Abasa 80:23

Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari)

Verse 24 — Surah Abasa 80:24

To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa

Verse 25 — Surah Abasa 80:25

Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa

Verse 26 — Surah Abasa 80:26

Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa

Verse 27 — Surah Abasa 80:27

Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta

Verse 28 — Surah Abasa 80:28

Verse 29 — Surah Abasa 80:29

Da zaitũni da itãcen dabĩno

Verse 30 — Surah Abasa 80:30

Da lambuna, mãsu yawan itãce

Verse 31 — Surah Abasa 80:31

Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi

Verse 32 — Surah Abasa 80:32

Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku

Verse 33 — Surah Abasa 80:33

To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo

Verse 34 — Surah Abasa 80:34

Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa

Verse 35 — Surah Abasa 80:35

Verse 36 — Surah Abasa 80:36

Da mãtarsa da ɗiyansa

Verse 37 — Surah Abasa 80:37

Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi

Verse 38 — Surah Abasa 80:38

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne

Verse 39 — Surah Abasa 80:39

Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra

Verse 40 — Surah Abasa 80:40

Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu

Verse 41 — Surah Abasa 80:41

Verse 42 — Surah Abasa 80:42

Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu)