Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 81 - At-Takwir
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah At-Takwir 81:1
Idan rãna aka shafe haskenta
Verse 2 — Surah At-Takwir 81:2
Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani)
Verse 3 — Surah At-Takwir 81:3
Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su
Verse 4 — Surah At-Takwir 81:4
Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba
Verse 5 — Surah At-Takwir 81:5
Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su
Verse 6 — Surah At-Takwir 81:6
Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta
Verse 7 — Surah At-Takwir 81:7
Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu
Verse 8 — Surah At-Takwir 81:8
Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta
Verse 9 — Surah At-Takwir 81:9
Sabõda wane laifi ne aka kashe ta
Verse 10 — Surah At-Takwir 81:10
Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su)
Verse 11 — Surah At-Takwir 81:11
Kuma idan sama aka fẽɗe ta
Verse 12 — Surah At-Takwir 81:12
Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
Verse 13 — Surah At-Takwir 81:13
Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita
Verse 14 — Surah At-Takwir 81:14
Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan)
Verse 15 — Surah At-Takwir 81:15
To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba
Verse 16 — Surah At-Takwir 81:16
Mãsu gudu suna ɓũya
Verse 17 — Surah At-Takwir 81:17
Da dare idan ya bãyar da bãya
Verse 18 — Surah At-Takwir 81:18
Da sãfiya idan ta yi lumfashi
Verse 19 — Surah At-Takwir 81:19
Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah
Verse 20 — Surah At-Takwir 81:20
Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi
Verse 21 — Surah At-Takwir 81:21
Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce
Verse 22 — Surah At-Takwir 81:22
Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne
Verse 23 — Surah At-Takwir 81:23
Kuma lalle ne, yã gan shi* a cikin sararin sama mabayyani
Verse 24 — Surah At-Takwir 81:24
Kuma shi, ga gaibi* bã mai rowa ba ne
Verse 25 — Surah At-Takwir 81:25
Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce
Verse 26 — Surah At-Takwir 81:26
Shin, a inã zã ku tafi
Verse 27 — Surah At-Takwir 81:27
Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai
Verse 28 — Surah At-Takwir 81:28
Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu
Verse 29 — Surah At-Takwir 81:29
Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda