Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 82 - Al-Infitar
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Infitar 82:1
Idan sama ta tsãge
Verse 2 — Surah Al-Infitar 82:2
Kuma idan taurãri suka wãtse
Verse 3 — Surah Al-Infitar 82:3
Kuma idan tẽkuna aka facce su
Verse 4 — Surah Al-Infitar 82:4
Kuma idan kaburbura aka tõne su
Verse 5 — Surah Al-Infitar 82:5
Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar
Verse 6 — Surah Al-Infitar 82:6
Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci
Verse 7 — Surah Al-Infitar 82:7
Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka
Verse 8 — Surah Al-Infitar 82:8
A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta
Verse 9 — Surah Al-Infitar 82:9
A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako
Verse 10 — Surah Al-Infitar 82:10
Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara
Verse 11 — Surah Al-Infitar 82:11
Mãsu daraja, marubũta
Verse 12 — Surah Al-Infitar 82:12
Sunã sanin abin da kuke aikatãwa
Verse 13 — Surah Al-Infitar 82:13
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima
Verse 14 — Surah Al-Infitar 82:14
Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm
Verse 15 — Surah Al-Infitar 82:15
Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako
Verse 16 — Surah Al-Infitar 82:16
Bã zã su faku daga gare ta ba
Verse 17 — Surah Al-Infitar 82:17
Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako
Verse 18 — Surah Al-Infitar 82:18
Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako
Verse 19 — Surah Al-Infitar 82:19
Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake