Back to Languages

Hausa - Chapter 83 - Al-Mutaffifin

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Mutaffifin 83:1

Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa

Verse 2 — Surah Al-Mutaffifin 83:2

Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu

Verse 3 — Surah Al-Mutaffifin 83:3

Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa

Verse 4 — Surah Al-Mutaffifin 83:4

Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba

Verse 5 — Surah Al-Mutaffifin 83:5

Domin yini mai girma

Verse 6 — Surah Al-Mutaffifin 83:6

Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta

Verse 7 — Surah Al-Mutaffifin 83:7

Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn

Verse 8 — Surah Al-Mutaffifin 83:8

Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn

Verse 9 — Surah Al-Mutaffifin 83:9

Wani ittãfi ne rubũtacce

Verse 10 — Surah Al-Mutaffifin 83:10

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa

Verse 11 — Surah Al-Mutaffifin 83:11

Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako

Verse 12 — Surah Al-Mutaffifin 83:12

Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi

Verse 13 — Surah Al-Mutaffifin 83:13

Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne

Verse 14 — Surah Al-Mutaffifin 83:14

A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu

Verse 15 — Surah Al-Mutaffifin 83:15

A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne

Verse 16 — Surah Al-Mutaffifin 83:16

Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne

Verse 17 — Surah Al-Mutaffifin 83:17

Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi

Verse 18 — Surah Al-Mutaffifin 83:18

A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna

Verse 19 — Surah Al-Mutaffifin 83:19

Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna

Verse 20 — Surah Al-Mutaffifin 83:20

Wani littãfi ne rubũtacce

Verse 21 — Surah Al-Mutaffifin 83:21

Muƙarrabai* suke halarta shi

Verse 22 — Surah Al-Mutaffifin 83:22

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima

Verse 23 — Surah Al-Mutaffifin 83:23

A kan karagu, suna ta kallo

Verse 24 — Surah Al-Mutaffifin 83:24

Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima

Verse 25 — Surah Al-Mutaffifin 83:25

Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta

Verse 26 — Surah Al-Mutaffifin 83:26

¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma

Verse 27 — Surah Al-Mutaffifin 83:27

Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake

Verse 28 — Surah Al-Mutaffifin 83:28

(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi

Verse 29 — Surah Al-Mutaffifin 83:29

Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya

Verse 30 — Surah Al-Mutaffifin 83:30

Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe

Verse 31 — Surah Al-Mutaffifin 83:31

Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci

Verse 32 — Surah Al-Mutaffifin 83:32

Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne

Verse 33 — Surah Al-Mutaffifin 83:33

Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu

Verse 34 — Surah Al-Mutaffifin 83:34

To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya

Verse 35 — Surah Al-Mutaffifin 83:35

A kan karagu, suna ta kallo

Verse 36 — Surah Al-Mutaffifin 83:36

Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa