Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 84 - Al-Inshiqaq
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Inshiqaq 84:1
Idan sama ta kẽce
Verse 2 — Surah Al-Inshiqaq 84:2
Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron
Verse 3 — Surah Al-Inshiqaq 84:3
Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta
Verse 4 — Surah Al-Inshiqaq 84:4
Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme
Verse 5 — Surah Al-Inshiqaq 84:5
Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren
Verse 6 — Surah Al-Inshiqaq 84:6
Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne
Verse 7 — Surah Al-Inshiqaq 84:7
To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa
Verse 8 — Surah Al-Inshiqaq 84:8
To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi
Verse 9 — Surah Al-Inshiqaq 84:9
Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha
Verse 10 — Surah Al-Inshiqaq 84:10
Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa
Verse 11 — Surah Al-Inshiqaq 84:11
To, zã shi dinga kiran halaka
Verse 12 — Surah Al-Inshiqaq 84:12
Kuma ya shiga sa'ĩr
Verse 13 — Surah Al-Inshiqaq 84:13
Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha
Verse 14 — Surah Al-Inshiqaq 84:14
Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba
Verse 15 — Surah Al-Inshiqaq 84:15
Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi
Verse 16 — Surah Al-Inshiqaq 84:16
To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba
Verse 17 — Surah Al-Inshiqaq 84:17
Da dare, da abin da ya ƙunsa
Verse 18 — Surah Al-Inshiqaq 84:18
Da watã idan (haskensa) ya cika
Verse 19 — Surah Al-Inshiqaq 84:19
Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli
Verse 20 — Surah Al-Inshiqaq 84:20
To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni
Verse 21 — Surah Al-Inshiqaq 84:21
Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u
Verse 22 — Surah Al-Inshiqaq 84:22
Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi
Verse 23 — Surah Al-Inshiqaq 84:23
Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa
Verse 24 — Surah Al-Inshiqaq 84:24
Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi
Verse 25 — Surah Al-Inshiqaq 84:25
Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa