Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 91 - Ash-Shams
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ash-Shams 91:1
Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta
Verse 2 — Surah Ash-Shams 91:2
Kuma da wata idan ya bi ta
Verse 3 — Surah Ash-Shams 91:3
Da yini a lõkacin da ya bayyana ta
Verse 4 — Surah Ash-Shams 91:4
Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta
Verse 5 — Surah Ash-Shams 91:5
Da sama da abin da ya gina ta
Verse 6 — Surah Ash-Shams 91:6
Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta
Verse 7 — Surah Ash-Shams 91:7
Da rai da abin da ya daidaita shi
Verse 8 — Surah Ash-Shams 91:8
Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa
Verse 9 — Surah Ash-Shams 91:9
Lalle ne wanda ya tsarkake* shi (rai) ya sãmi babban rabo
Verse 10 — Surah Ash-Shams 91:10
Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe* shi (da laifi) ya tãɓe
Verse 11 — Surah Ash-Shams 91:11
Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu
Verse 12 — Surah Ash-Shams 91:12
A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu)
Verse 13 — Surah Ash-Shams 91:13
Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta
Verse 14 — Surah Ash-Shams 91:14
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi)
Verse 15 — Surah Ash-Shams 91:15
Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar)