Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 90 - Al-Balad
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Balad 90:1
Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari* ba
Verse 2 — Surah Al-Balad 90:2
Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari
Verse 3 — Surah Al-Balad 90:3
Da mahaifi da abin da ya haifa
Verse 4 — Surah Al-Balad 90:4
Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala
Verse 5 — Surah Al-Balad 90:5
Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa
Verse 6 — Surah Al-Balad 90:6
Yana cẽwa "Na* halakarda dũkiya mai yawa
Verse 7 — Surah Al-Balad 90:7
Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba
Verse 8 — Surah Al-Balad 90:8
Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba
Verse 9 — Surah Al-Balad 90:9
Da harshe, da leɓɓa biyu
Verse 10 — Surah Al-Balad 90:10
Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi* biyu ba
Verse 11 — Surah Al-Balad 90:11
To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba
Verse 12 — Surah Al-Balad 90:12
Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã
Verse 13 — Surah Al-Balad 90:13
Ita ce fansar wuyan bãwa
Verse 14 — Surah Al-Balad 90:14
Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa
Verse 15 — Surah Al-Balad 90:15
Ga marãya ma'abũcin zumunta
Verse 16 — Surah Al-Balad 90:16
Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya
Verse 17 — Surah Al-Balad 90:17
Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi
Verse 18 — Surah Al-Balad 90:18
Waɗannan ne ma'abũta albarka
Verse 19 — Surah Al-Balad 90:19
Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci
Verse 20 — Surah Al-Balad 90:20
A kansu akwai wata wuta abar kullewa