Back to Languages

Hausa - Chapter 89 - Al-Fajr

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Fajr 89:1

Inã rantsuwa da alfijiri

Verse 2 — Surah Al-Fajr 89:2

Verse 3 — Surah Al-Fajr 89:3

Da (adadi na) cikã da (na) mãrã

Verse 4 — Surah Al-Fajr 89:4

Da dare idan yana shũɗewa

Verse 5 — Surah Al-Fajr 89:5

Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)

Verse 6 — Surah Al-Fajr 89:6

Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba

Verse 7 — Surah Al-Fajr 89:7

Iramawa mãsu sakon* ƙĩrar jiki

Verse 8 — Surah Al-Fajr 89:8

Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya)

Verse 9 — Surah Al-Fajr 89:9

Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi* suka yi gidãje

Verse 10 — Surah Al-Fajr 89:10

Da Fir'auna mai turãku

Verse 11 — Surah Al-Fajr 89:11

Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa

Verse 12 — Surah Al-Fajr 89:12

Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu

Verse 13 — Surah Al-Fajr 89:13

Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba

Verse 14 — Surah Al-Fajr 89:14

Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka

Verse 15 — Surah Al-Fajr 89:15

To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni

Verse 16 — Surah Al-Fajr 89:16

Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni

Verse 17 — Surah Al-Fajr 89:17

A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya

Verse 18 — Surah Al-Fajr 89:18

Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci

Verse 19 — Surah Al-Fajr 89:19

Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa

Verse 20 — Surah Al-Fajr 89:20

Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa

Verse 21 — Surah Al-Fajr 89:21

A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai

Verse 22 — Surah Al-Fajr 89:22

Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu

Verse 23 — Surah Al-Fajr 89:23

Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi

Verse 24 — Surah Al-Fajr 89:24

Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata

Verse 25 — Surah Al-Fajr 89:25

To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah

Verse 26 — Surah Al-Fajr 89:26

Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa

Verse 27 — Surah Al-Fajr 89:27

Yã kai rai mai natsuwa

Verse 28 — Surah Al-Fajr 89:28

Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira)

Verse 29 — Surah Al-Fajr 89:29

Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya)

Verse 30 — Surah Al-Fajr 89:30

Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira)