Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 88 - Al-Ghashiyah
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Ghashiyah 88:1
Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka
Verse 2 — Surah Al-Ghashiyah 88:2
Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne
Verse 3 — Surah Al-Ghashiyah 88:3
Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya
Verse 4 — Surah Al-Ghashiyah 88:4
Zã su shiga wata wuta mai zãfi
Verse 5 — Surah Al-Ghashiyah 88:5
Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa
Verse 6 — Surah Al-Ghashiyah 88:6
Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi
Verse 7 — Surah Al-Ghashiyah 88:7
Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba
Verse 8 — Surah Al-Ghashiyah 88:8
Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne
Verse 9 — Surah Al-Ghashiyah 88:9
Game da aikinsu, masu yarda ne
Verse 10 — Surah Al-Ghashiyah 88:10
(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya
Verse 11 — Surah Al-Ghashiyah 88:11
Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta
Verse 12 — Surah Al-Ghashiyah 88:12
A cikinta akwai marmaro mai gudãna
Verse 13 — Surah Al-Ghashiyah 88:13
A cikinta akwai gadãje maɗaukaka
Verse 14 — Surah Al-Ghashiyah 88:14
Da kõfuna ar'aje
Verse 15 — Surah Al-Ghashiyah 88:15
Da filõli* jẽre
Verse 16 — Surah Al-Ghashiyah 88:16
Da katifu shimfiɗe
Verse 17 — Surah Al-Ghashiyah 88:17
Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su
Verse 18 — Surah Al-Ghashiyah 88:18
Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta
Verse 19 — Surah Al-Ghashiyah 88:19
Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su
Verse 20 — Surah Al-Ghashiyah 88:20
Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta
Verse 21 — Surah Al-Ghashiyah 88:21
sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai
Verse 22 — Surah Al-Ghashiyah 88:22
Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba
Verse 23 — Surah Al-Ghashiyah 88:23
Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta
Verse 24 — Surah Al-Ghashiyah 88:24
To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma
Verse 25 — Surah Al-Ghashiyah 88:25
Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take
Verse 26 — Surah Al-Ghashiyah 88:26
Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi