Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 87 - Al-Ala
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Ala 87:1
Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka
Verse 2 — Surah Al-Ala 87:2
Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar
Verse 3 — Surah Al-Ala 87:3
Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri)
Verse 4 — Surah Al-Ala 87:4
Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã
Verse 5 — Surah Al-Ala 87:5
Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa
Verse 6 — Surah Al-Ala 87:6
Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba
Verse 7 — Surah Al-Ala 87:7
Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye
Verse 8 — Surah Al-Ala 87:8
Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi
Verse 9 — Surah Al-Ala 87:9
Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni
Verse 10 — Surah Al-Ala 87:10
Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna
Verse 11 — Surah Al-Ala 87:11
Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta
Verse 12 — Surah Al-Ala 87:12
Wanda zai shiga wutar da tã fi girma
Verse 13 — Surah Al-Ala 87:13
Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba
Verse 14 — Surah Al-Ala 87:14
Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo
Verse 15 — Surah Al-Ala 87:15
Kuma ya ambaci sũnan* Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla
Verse 16 — Surah Al-Ala 87:16
Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya
Verse 17 — Surah Al-Ala 87:17
Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa
Verse 18 — Surah Al-Ala 87:18
Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko
Verse 19 — Surah Al-Ala 87:19
Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã