Back to Languages

Hausa - Chapter 86 - At-Tariq

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah At-Tariq 86:1

Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare

Verse 2 — Surah At-Tariq 86:2

To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare

Verse 3 — Surah At-Tariq 86:3

Shi ne taurãron nan mai tsananin haske

Verse 4 — Surah At-Tariq 86:4

Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro

Verse 5 — Surah At-Tariq 86:5

To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi

Verse 6 — Surah At-Tariq 86:6

An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna

Verse 7 — Surah At-Tariq 86:7

Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji

Verse 8 — Surah At-Tariq 86:8

Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne

Verse 9 — Surah At-Tariq 86:9

Rãnar da ake jarrabawar asirai

Verse 10 — Surah At-Tariq 86:10

Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah)

Verse 11 — Surah At-Tariq 86:11

Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa

Verse 12 — Surah At-Tariq 86:12

Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa

Verse 13 — Surah At-Tariq 86:13

Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki

Verse 14 — Surah At-Tariq 86:14

Kuma shĩ bã bananci* bane

Verse 15 — Surah At-Tariq 86:15

Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai

Verse 16 — Surah At-Tariq 86:16

Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi

Verse 17 — Surah At-Tariq 86:17

Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu