Back to Languages

Hausa - Chapter 93 - Ad-Duhaa

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ad-Duhaa 93:1

Inã rantsuwa da hantsi

Verse 2 — Surah Ad-Duhaa 93:2

Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa)

Verse 3 — Surah Ad-Duhaa 93:3

Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba

Verse 4 — Surah Ad-Duhaa 93:4

Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko

Verse 5 — Surah Ad-Duhaa 93:5

Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda

Verse 6 — Surah Ad-Duhaa 93:6

Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma

Verse 7 — Surah Ad-Duhaa 93:7

Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai

Verse 8 — Surah Ad-Duhaa 93:8

Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka

Verse 9 — Surah Ad-Duhaa 93:9

Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi

Verse 10 — Surah Ad-Duhaa 93:10

Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa

Verse 11 — Surah Ad-Duhaa 93:11

Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya)