Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 94 - Ash-Sharh
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ash-Sharh 94:1
Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)
Verse 2 — Surah Ash-Sharh 94:2
Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe
Verse 3 — Surah Ash-Sharh 94:3
Wanda ya nauyayi bãyanka
Verse 4 — Surah Ash-Sharh 94:4
Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka
Verse 5 — Surah Ash-Sharh 94:5
To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi
Verse 6 — Surah Ash-Sharh 94:6
Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi
Verse 7 — Surah Ash-Sharh 94:7
Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah)
Verse 8 — Surah Ash-Sharh 94:8
Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi