Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 95 - At-Tin
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah At-Tin 95:1
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn
Verse 2 — Surah At-Tin 95:2
Da Dũr Sĩnĩna
Verse 3 — Surah At-Tin 95:3
Da wannan gari* amintacce
Verse 4 — Surah At-Tin 95:4
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa
Verse 5 — Surah At-Tin 95:5
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
Verse 6 — Surah At-Tin 95:6
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa
Verse 7 — Surah At-Tin 95:7
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)
Verse 8 — Surah At-Tin 95:8
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba