Back to Languages

Hausa - Chapter 96 - Al-Alaq

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Alaq 96:1

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta

Verse 2 — Surah Al-Alaq 96:2

Ya hahitta mutum daga gudan jini

Verse 3 — Surah Al-Alaq 96:3

Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci

Verse 4 — Surah Al-Alaq 96:4

Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami

Verse 5 — Surah Al-Alaq 96:5

Ya sanar da mutum abin da bai sani ba

Verse 6 — Surah Al-Alaq 96:6

A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu)

Verse 7 — Surah Al-Alaq 96:7

Dõmin yã ga kansa, yã wadãta

Verse 8 — Surah Al-Alaq 96:8

Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take

Verse 9 — Surah Al-Alaq 96:9

Shin, kã ga wanda ke hana

Verse 10 — Surah Al-Alaq 96:10

Bãwã idan yã yi salla

Verse 11 — Surah Al-Alaq 96:11

Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya

Verse 12 — Surah Al-Alaq 96:12

Ko ya yi umurni da taƙawa

Verse 13 — Surah Al-Alaq 96:13

Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya

Verse 14 — Surah Al-Alaq 96:14

Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani

Verse 15 — Surah Al-Alaq 96:15

A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa

Verse 16 — Surah Al-Alaq 96:16

Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi

Verse 17 — Surah Al-Alaq 96:17

Sai ya kirayi ƙungiyarsa

Verse 18 — Surah Al-Alaq 96:18

Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma)

Verse 19 — Surah Al-Alaq 96:19

A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka)