Back to Languages

Hausa - Chapter 97 - Al-Qadr

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Qadr 97:1

Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)

Verse 2 — Surah Al-Qadr 97:2

To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari

Verse 3 — Surah Al-Qadr 97:3

Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu

Verse 4 — Surah Al-Qadr 97:4

Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni

Verse 5 — Surah Al-Qadr 97:5

Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri