Back to Languages

Hausa - Chapter 54 - Al-Qamar

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Qamar 54:1

Sa'a ta yi kusa, kuma wata *ya tsage

Verse 2 — Surah Al-Qamar 54:2

Kuma idan sun ga wata aya, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dogewa

Verse 3 — Surah Al-Qamar 54:3

Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zuciyarsu, alhali kuwa kowane al'amari (wanda suke son su ture daga Annabi) an tabbatar da shi

Verse 4 — Surah Al-Qamar 54:4

Kuma lalle, abin da yake akwai tsawatarwa a cikinsa na labaraiya zo musu

Verse 5 — Surah Al-Qamar 54:5

Hikima cikakka! Sai dai abubuwan gargaɗi ba su amfani

Verse 6 — Surah Al-Qamar 54:6

Saboda haka, ka bar su! Ranar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama

Verse 7 — Surah Al-Qamar 54:7

¡asƙantattu ga idanunsu za su fito daga kaburburansu, kamar dai su fari ne waɗandasuka watse

Verse 8 — Surah Al-Qamar 54:8

Suna gaggawar tafiya zuwa ga mai kiran, kafirai na cewa, "Wannan yini ne mai wuya

Verse 9 — Surah Al-Qamar 54:9

Mutanen Nuhu sun ƙaryata, a gabaninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsawace shi

Verse 10 — Surah Al-Qamar 54:10

Saboda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle ni, an rinjaye ni, sai Ka yi taimako

Verse 11 — Surah Al-Qamar 54:11

Sai Muka buɗe kofofin sama da ruwa mai zuba

Verse 12 — Surah Al-Qamar 54:12

Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasa ta zama idanun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi

Verse 13 — Surah Al-Qamar 54:13

Kuma Muka ɗauke Nuhu a kan (jirgi) na alluna da ƙusoshi

Verse 14 — Surah Al-Qamar 54:14

Tana gudana, a kan idanun Mu, domin sakamako ga wanda aka yi wa kafircin

Verse 15 — Surah Al-Qamar 54:15

Kuma lalle, Mun bar ta ta zama aya. To, Shin, akwai mai tunani

Verse 16 — Surah Al-Qamar 54:16

To, yaya azaba Ta take da gargaɗi Na

Verse 17 — Surah Al-Qamar 54:17

Kuma lalle ne, haƙikƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, domin tunawa. To, shin, akwai mai tunawa

Verse 18 — Surah Al-Qamar 54:18

Adawa sun ƙaryata, to, yaya azabaTa take, da gargaɗi Na

Verse 19 — Surah Al-Qamar 54:19

Lalle Mu, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahisa mai dogewa

Verse 20 — Surah Al-Qamar 54:20

Tana fizgar mutane kamar dai su kututturan dabino tumɓukakku ne

Verse 21 — Surah Al-Qamar 54:21

To, yaya azaba Ta take da gargaɗi Na

Verse 22 — Surah Al-Qamar 54:22

Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, domin tunawa. To, shin, akwai mai tunawa

Verse 23 — Surah Al-Qamar 54:23

Samudawa sun ƙaryata game da gargaɗin

Verse 24 — Surah Al-Qamar 54:24

Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bi shi! Lalle mu a lokacin, haƙiƙa mun shiga wata ɓata da hauka

Verse 25 — Surah Al-Qamar 54:25

Shin, an jefa masa Manzancin ne, a tsakaninmu? A'a, shi dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai

Verse 26 — Surah Al-Qamar 54:26

Za su sani a gobe, wane ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan

Verse 27 — Surah Al-Qamar 54:27

Lalle Mu, masu aikawa da raƙumar* ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri

Verse 28 — Surah Al-Qamar 54:28

Kuma ka ba su labari cewa ruwa rababbe ne a tsakaninsu (da raƙumar), kowane sha, mai shi yana halartar sa

Verse 29 — Surah Al-Qamar 54:29

Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya soke ta

Verse 30 — Surah Al-Qamar 54:30

To, yaya azabaTa take da gargaɗi Na

Verse 31 — Surah Al-Qamar 54:31

Lalle Mu, Mun aika tsawa guda a kansu, sai suka kasance kamar yayin mai shinge

Verse 32 — Surah Al-Qamar 54:32

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, domin tunawa. To, shin, akwai mai tunawa

Verse 33 — Surah Al-Qamar 54:33

Mutanen Luɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi

Verse 34 — Surah Al-Qamar 54:34

Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, face mabiyan Luɗu, Mun tsirar da su a lokacin asuba

Verse 35 — Surah Al-Qamar 54:35

Saboda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke saka wa wanda ya gode

Verse 36 — Surah Al-Qamar 54:36

Kuma lalle, haƙiƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin

Verse 37 — Surah Al-Qamar 54:37

Kuma lalle haƙiƙa, su, sun neme shi ta wajen baƙinsa, sai Muka shafe idanunsu. "To, ku ɗanɗani azabaTa da gargaɗi Na

Verse 38 — Surah Al-Qamar 54:38

Kuma lalle, haƙiƙa, wata azaba matabbaciya ta waye musu gari da yaƙi, tun da safe

Verse 39 — Surah Al-Qamar 54:39

To, ku ɗanɗani azabaTa da gargaɗi Na

Verse 40 — Surah Al-Qamar 54:40

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani domin tunawa. To, shin, akwai mai tunawa

Verse 41 — Surah Al-Qamar 54:41

Kuma lalle, haƙiƙa, gargaɗin ya je wa mabiyan Fir'auna

Verse 42 — Surah Al-Qamar 54:42

Sun ƙaryata game da ayoyin Mu, dukansu sai Muka kama su, irin kamun Mabuwayi, Mai ikon yi

Verse 43 — Surah Al-Qamar 54:43

Shin, kafiranku ne mafi alheri daga waɗancan, ko kuwa kuna da wata bara'a a cikin littattafai

Verse 44 — Surah Al-Qamar 54:44

Ko za su ce: "Mu duka masu haɗa ƙarfi ne domin cin nasara

Verse 45 — Surah Al-Qamar 54:45

Za a karya* taron, kuma su juya baya domin gudu

Verse 46 — Surah Al-Qamar 54:46

A'a, Sa'a ita ce lokacin wa'adinsu, kuma Sa'ar ta fi tsananin masifa, kuma ta fiɗaci

Verse 47 — Surah Al-Qamar 54:47

Lalle ne, masu laifi suna a cikin ɓata da hauka

Verse 48 — Surah Al-Qamar 54:48

Ranar da za a ja su a cikin wuta a kan fuskokinsu. "Ku ɗanɗani shafar wutar Saƙar

Verse 49 — Surah Al-Qamar 54:49

Lalle Mu, kowane irin abu Mun halitta shi a kan tsari

Verse 50 — Surah Al-Qamar 54:50

Kuma umurnin Mu bai zamo ba face da kalma ɗaya, kamar walƙawar ido

Verse 51 — Surah Al-Qamar 54:51

Kuma lalle ne haƙiƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunani

Verse 52 — Surah Al-Qamar 54:52

Kuma kowane abu, da suka aikata shi, yana a cikin littattafai

Verse 53 — Surah Al-Qamar 54:53

Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne

Verse 54 — Surah Al-Qamar 54:54

Lalle masu taƙawa suna a cikin gidajen Aljanna da koguna

Verse 55 — Surah Al-Qamar 54:55

A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa