Back to Languages

Hausa - Chapter 56 - Al-Waqiah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Waqiah 56:1

Idan mai aukuwa ta auku

Verse 2 — Surah Al-Waqiah 56:2

Babu wani (rai) mai ƙaryatawa ga aukuwarta

Verse 3 — Surah Al-Waqiah 56:3

(Ita) mai ƙasƙantawa ce, mai ɗaukakawa

Verse 4 — Surah Al-Waqiah 56:4

Idan aka girgiza ƙasa girgizwa

Verse 5 — Surah Al-Waqiah 56:5

Kuma aka niƙe duwatsu, niƙewa

Verse 6 — Surah Al-Waqiah 56:6

Sai suka kasance ƙura da ake watsarwa

Verse 7 — Surah Al-Waqiah 56:7

Kuma kun kasance nau'i uku

Verse 8 — Surah Al-Waqiah 56:8

Watau mazowa dama*. Mene ne mazowa dama

Verse 9 — Surah Al-Waqiah 56:9

Da mazowa hagu. Mene ne mazowa hagu

Verse 10 — Surah Al-Waqiah 56:10

Da waɗanda suka tsere. Su wɗanda suka tseren nan

Verse 11 — Surah Al-Waqiah 56:11

Waɗancan, su ne waɗanda aka kusantar

Verse 12 — Surah Al-Waqiah 56:12

A ckin Aljannar ni'ima

Verse 13 — Surah Al-Waqiah 56:13

Jama'a ne daga mutanen farko

Verse 14 — Surah Al-Waqiah 56:14

Da kaɗan daga mutanen ƙarshe

Verse 15 — Surah Al-Waqiah 56:15

(Suna) a kan wasu gadaje saƙaƙƙu

Verse 16 — Surah Al-Waqiah 56:16

Suna gincire a kansu, suna masu kallon juna

Verse 17 — Surah Al-Waqiah 56:17

Wasu yara samari na dindindin gewaya a kansu

Verse 18 — Surah Al-Waqiah 56:18

Da wasu kofuna da shantula da hinjalai daga (giya) mai ɓuɓɓuga

Verse 19 — Surah Al-Waqiah 56:19

Ba a sanya musu ciwon jiri saboda ita, kuma ba su buguwa

Verse 20 — Surah Al-Waqiah 56:20

Da wasu 'ya'yan itacen marmari daga irin waɗanda suke zaɓe

Verse 21 — Surah Al-Waqiah 56:21

Da naman tsuntsaye daga wanda suke ganin sha'awa

Verse 22 — Surah Al-Waqiah 56:22

Da wasu mata masu fararen idanu da girmansu

Verse 23 — Surah Al-Waqiah 56:23

Kamar misalan lu'ulu'u wanda aka ɓoye

Verse 24 — Surah Al-Waqiah 56:24

A kan sakamakon, domin abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 25 — Surah Al-Waqiah 56:25

Ba su jin wata yasassar magana a cikinta, kuma ba su jin sun yi laifi

Verse 26 — Surah Al-Waqiah 56:26

Sai dai wata magana (mai daɗi): Salamun, Salamun

Verse 27 — Surah Al-Waqiah 56:27

Da mazowa dama. Mene ne mazowa dama

Verse 28 — Surah Al-Waqiah 56:28

(Suna) a cikin itacen magarya maras ƙaya

Verse 29 — Surah Al-Waqiah 56:29

Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya

Verse 30 — Surah Al-Waqiah 56:30

Da wata inuwa miƙaƙƙiya

Verse 31 — Surah Al-Waqiah 56:31

Da wani ruwa mai gudana

Verse 32 — Surah Al-Waqiah 56:32

Da wasu 'ya'yan itacen marmari masu yawa

Verse 33 — Surah Al-Waqiah 56:33

Ba su yankewa kuma ba a hana su

Verse 34 — Surah Al-Waqiah 56:34

Da wasu shimfiɗu maɗaukaka

Verse 35 — Surah Al-Waqiah 56:35

Lalle Mu, Mun ƙaga halittarsu ƙagawa

Verse 36 — Surah Al-Waqiah 56:36

Sa'an nan Muka sanya su budurwai

Verse 37 — Surah Al-Waqiah 56:37

Masu son mazansu, a cikin tsara ɗaya

Verse 38 — Surah Al-Waqiah 56:38

Verse 39 — Surah Al-Waqiah 56:39

Wata ƙungiya ce daga mutanen farko

Verse 40 — Surah Al-Waqiah 56:40

Da wata ƙungiya daga mutanen ƙarshe

Verse 41 — Surah Al-Waqiah 56:41

Mazowa hagu, Mene ne mazowa hagu

Verse 42 — Surah Al-Waqiah 56:42

Suna a cikin wata iskar zafi da wani ruwan zafi

Verse 43 — Surah Al-Waqiah 56:43

Da wata inuwa ta hayaƙi mai baƙi

Verse 44 — Surah Al-Waqiah 56:44

Ba mai sanyi ba, kuma ba mai wata ni'ima ba

Verse 45 — Surah Al-Waqiah 56:45

Lalle su, sun kasance a gabanin wannan waɗanda aka jiyar daɗi

Verse 46 — Surah Al-Waqiah 56:46

Kuma sun kasance suna dogewa a kan mummunan zunubi mai girma

Verse 47 — Surah Al-Waqiah 56:47

Kuma sun kasance suna cewa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓaya da ƙasusuwa shin lalle mu waɗanda za a koma rayarwa ne haƙiƙatan

Verse 48 — Surah Al-Waqiah 56:48

Shin, kuma da ubanninmu na farko

Verse 49 — Surah Al-Waqiah 56:49

Ka ce: "Lalle mutanen farko da na ƙarshe

Verse 50 — Surah Al-Waqiah 56:50

Tabbas, waɗanda ake tarawa ne a cikin wani yini sananne

Verse 51 — Surah Al-Waqiah 56:51

Sa'an nan lalle ku, ya ku ɓatattu, masu ƙaryatawa

Verse 52 — Surah Al-Waqiah 56:52

Lalle masu ci ne daga wata itaciya ta zaƙƙum (ɗanyen wuta)

Verse 53 — Surah Al-Waqiah 56:53

Har za ku zama masu cika cikunna daga gare ta

Verse 54 — Surah Al-Waqiah 56:54

Sa'an nan kuma masu sha ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zafi

Verse 55 — Surah Al-Waqiah 56:55

Ku zama masu sha irin shan raƙuma masu ƙishirwa

Verse 56 — Surah Al-Waqiah 56:56

Wannan ita ce liyafarsu a ranar sakamako

Verse 57 — Surah Al-Waqiah 56:57

Mu ne Muka halitta ku, to, don me ba za ku gaskata ba

Verse 58 — Surah Al-Waqiah 56:58

Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi

Verse 59 — Surah Al-Waqiah 56:59

Shin ku ne kuke halitta shi, ko kuwa mu ne Masu halittawa

Verse 60 — Surah Al-Waqiah 56:60

Mu ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakaninku, kuma ba Mu zama Masu gajiyawa* ba

Verse 61 — Surah Al-Waqiah 56:61

A kan Mu musanya waɗansu (mutane) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba

Verse 62 — Surah Al-Waqiah 56:62

Kuma lalle, ne haƙiƙa, kun san halittar farko, to, don me ba za ku yi tunani ba

Verse 63 — Surah Al-Waqiah 56:63

Shin, kuma kun ga abin da kuke nomawa

Verse 64 — Surah Al-Waqiah 56:64

Shin, ku ne ke tsirar da shi ko kuwa Mu ne Masu tsirarwa

Verse 65 — Surah Al-Waqiah 56:65

Da Muna so lalle, da Mun sanya shi busasshiyar ciyawa, sai ku yini kuna mamakin baƙin ciki

Verse 66 — Surah Al-Waqiah 56:66

(Kuna cewa) "Lalle haƙiƙa an aza mana tara

Verse 67 — Surah Al-Waqiah 56:67

A'a, mun dai zama waɗanda aka hana wa

Verse 68 — Surah Al-Waqiah 56:68

Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha

Verse 69 — Surah Al-Waqiah 56:69

Shin, ku ne kuke saukar da shi daga girgije, ko kuwa Mune Masu saukarwa

Verse 70 — Surah Al-Waqiah 56:70

Da Mun so, da Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me ba ku godewa

Verse 71 — Surah Al-Waqiah 56:71

Shin, kuma kun ga wuta wannan da kuke ƙyastawa

Verse 72 — Surah Al-Waqiah 56:72

Shin, ku ne kuke ƙaga halittar itaciyarta, ko kuwa Mu ne Masu ƙagawa

Verse 73 — Surah Al-Waqiah 56:73

Mu ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin daɗi ga matafiya a cikin jeji

Verse 74 — Surah Al-Waqiah 56:74

Sai ka tsarkake sunan Ubangijinka Mai girma

Verse 75 — Surah Al-Waqiah 56:75

To, ba sai Na yi rantsuwa ba da lokutan faɗuwar taurari

Verse 76 — Surah Al-Waqiah 56:76

Kuma lalle ne' haƙiƙa, rantsuwa ce mai girma, da kun sani

Verse 77 — Surah Al-Waqiah 56:77

Lalle shi (wannan littafi), haƙiƙa, abin karantawa ne mai daraja

Verse 78 — Surah Al-Waqiah 56:78

A cikin wani littafi tsararre

Verse 79 — Surah Al-Waqiah 56:79

Babu mai shafa shi face waɗanda aka tsarkake

Verse 80 — Surah Al-Waqiah 56:80

Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta

Verse 81 — Surah Al-Waqiah 56:81

Shin, to, wannan labarin ne kuke masu wulakantawa

Verse 82 — Surah Al-Waqiah 56:82

Kuma kuna sanya arzikinku (game da shi) lalle ku, ku ƙaryata (shi)

Verse 83 — Surah Al-Waqiah 56:83

To, don me idan rai ya kai ga maƙoshi? (Kusa da mutuwa)

Verse 84 — Surah Al-Waqiah 56:84

Alhali kuwa ku, a loklcin nan, kuna kallo

Verse 85 — Surah Al-Waqiah 56:85

Kuma Mu ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma ku ba ku gani

Verse 86 — Surah Al-Waqiah 56:86

To, don me in dai kun kasance ba waɗanda za a yi wa sakamako ba

Verse 87 — Surah Al-Waqiah 56:87

Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance masu gaskiya

Verse 88 — Surah Al-Waqiah 56:88

To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta

Verse 89 — Surah Al-Waqiah 56:89

Sai hutawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima

Verse 90 — Surah Al-Waqiah 56:90

Kuma amma idan ya kasance daga mazowa dama

Verse 91 — Surah Al-Waqiah 56:91

Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazowa dama

Verse 92 — Surah Al-Waqiah 56:92

Kuma amma idan ya kasance daga masu ƙaryatawar, ɓatattun

Verse 93 — Surah Al-Waqiah 56:93

Sai wata liyafa ta ruwan zafi

Verse 94 — Surah Al-Waqiah 56:94

Verse 95 — Surah Al-Waqiah 56:95

Lalle wannan, haƙiƙa, ita ce gaskiya ta yaƙini

Verse 96 — Surah Al-Waqiah 56:96

Saboda haka, ka tsarkake* sunan Ubangijinka, Mai karimci