Shi ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwanuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yana sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shi yana tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatawa
Ku yi imani da Allah da Manzon Sa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku a cikinsa (na dukiya). To, waɗannan da suka yi imani daga cikinku, kuma suka ciyar, suna da wani sakamako mai girma
kuma me ya same ku, ba za ku yi imani ba da Allah, alhali kuwa manzon Sa na kiran ku domin ku yi imani da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cewa za ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance* masu imani
Shi ne wanda ke sassaukar da ayoyi bayyanannu ga Bawan Sa, domin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙiƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai jin ƙai
Kuma me ya same ku, ba za ku ciyar ba domin ɗaukaka kalmar Allah, alhali kuwa gadon sammai da ƙasa na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabanin cin nasara, kuma ya yi yaƙi daga cikinku, ba ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafifita girman daraja* bisa ga waɗanda suka ciyar daga baya kuma suka yi yaƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatawa
Ranar da za ka ga muminai maza da muminai mata haskensu na tafiya a gaba gare su, da kuma dama gare su. (Ana ce musu) "Bushararku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu. Wannan, shi ne babban rabo mai girma
Ranar da munafikai maza da munafikai mata ke cewa waɗanda suka yi imani: "Ku dube mu, mu yi makamashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku koma a bayanku, domin ku nemo wani haske." Sai a danne a tsakaninsu da wani garu yana da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bayansa daga wajensa azaba take
Suna kiran su, "Ashe, ba tare muke da ku ba?" Su ce: "I, amma ku, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masifa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gurace-gurace sun ruɗe ku, har umurnin Allah ya je muku, kumamaruɗi ya ruɗe ku game da Allah
To, a yau ba za a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma ba za a karɓa daga waɗanda suka kafirta ba. Makomarku wuta ce, ita ce mai dacewa da ku, kuma makomarku ɗin nan ta munana
Shin, lokaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi imani* zukatansu su yi tawalu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littafi a gabanin haka, sai zamani ya yi tsawo a kansu, saboda haka zukatansu suka ƙeƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fasiƙai ne
Kuma waɗanda suka yi imani da Allah da Mazannin Sa waɗannan su ne kamalar gaskatawa kuma su ne masu shahada awurin Ubangjinsu. suna da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ayoyin Mu, waɗannan su ne'yan Jahim
Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakaninku da gasar wadata ta dukiya da ɗiya, kamar misalin shuka wadda yabanyarta ta bayar da sha'awa ga manoma, sa'an nan ta ƙeƙashe, har ka ganta ta zama rawaya sa'an nan ta koma rauno. Kuma, alamra akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da yarda. Kuma rayuwar duniya ba ta zama ba face ɗan jin daɗin ruɗi kawai
Ku yi tsere zuwa ga (neman) gafara daga Ubangjinku, da Aljanna faɗinta kamar faɗin sama da ƙasa ne, an yi tattalinta domin waɗanda suka yi imani da Allah da Manzannin Sa. Wannan falalar Allah ce, Yana bayar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma
Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya ba ku. Kuma Allah ba Ya son dukkan mai taƙama, mai alfahari
Haƙiƙa, lalle Mun aiko Manzannin Mu da hujjoji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littafi da sikeli tare da su domin mutane su tsayu da adalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe,* a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfani ga mutane, kuma domin Allah Ya san mai taimakon Sa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwayi
Kuma haƙiƙa, lalle, Mun aiki Nuhu da Ibrahim, kuma Muka sanya Annabci da Littifi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai neman shiryuwa, kuma masu yawa daga cikinsu fasiƙai ne
Sa'an nan Muka biyar a bayansu* da Manzannin Mu; kuma Muka biyar da isa ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukatan waɗanda suka bi shi, da ruhbananci* wanda suka ƙaga, shi, ba Mu rubuta shi ba a kansu, face dai (Mun rubuta musu neman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarewarsa ba, saboda haka Muka bai wa waɗanda suka yi imani daga cikinsu sakamakonsu kuma masu yawa daga cikinsu fasiƙai ne)
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi imani da Manzon Sa* Ya ba ku rabo biyu daga rahamar Sa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gafarta muku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai rahama
Domin kada *mutanen Littafi su san cewa lalle ba su da ikon yi ga kome na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yana bayar da ita ga wanda Ya so (wannan jahilci ya hana su imani). Kuma Alah Mai falala ne mai girma