Back to Languages

Hausa - Chapter 58 - Al-Mujadila

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Mujadila 58:1

Lalle Alla Ya ji maganar* wadda ke yi maka jayayya game da mijinta, tana kai ƙara ga Allah, kuma Allah na jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani

Verse 2 — Surah Al-Mujadila 58:2

Waɗanda ke yin zihari daga cikinku game da matansu, sumatan nan ba uwayensu ba ne, babu uwayensu face waɗanda suka haife su. Lalle su, suna faɗar abin ƙyama na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙiƙa Mai yafewa ne, Mai gafara

Verse 3 — Surah Al-Mujadila 58:3

Waɗanda ke yin zihari game da matansu, sa'an nan su koma wa abin da suka faɗa, to, akwai 'yanta wuya a gabanin su shafi juna. Wannan ana yi muku wa'azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa

Verse 4 — Surah Al-Mujadila 58:4

To, wanda bai samu ba, sai azumin wata biyu jere a gabanin su shafi juna, sa'an nan wanda bai sami ikon yi ba, to, sai ciyar da miskinai sittin. Wannan domin ku yi imani da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddodin Allah ne. Kuma kafirai, suna da azaba mai raɗadi

Verse 5 — Surah Al-Mujadila 58:5

Lalle waɗanda ke saɓa wa Allah da ManzonSa, an wulakanta su kamar yadda aka wulakantar da waɗanda ke a gabaninsu, kuma lalle Mun saukar da ayoyi bayyanannu, kuma kafirai na da azaba mai wulakantawa

Verse 6 — Surah Al-Mujadila 58:6

Ranar da Allah zai tayar da su gaba ɗaya, sa'an nan Ya ba su labari game da abin da suka aikata, Allah Ya lissafa shi, alhali kuwa su, sun manta da shi, kuma a kan kome Allah Halartacce ne

Verse 7 — Surah Al-Mujadila 58:7

Ashe, ba ka ga cewa lalle Allah Yana sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata ganawa* ta mutum uku ba za ta kasance ba face Allah Shi ne na huɗu ɗinta, kuma babu ta mutum biyar face Shi ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kasa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa face Shi Yana tare da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya ba su labari game da abin da suka aikata a Ranar ¡iyama. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kome

Verse 8 — Surah Al-Mujadila 58:8

Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganawar, sa'an nan suna koma wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma suna ganawa game da zunubi da zalunci da saɓa wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma suna cewa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi mana azaba saboda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, za su shigeta. Saboda haka makomarsu ta munana

Verse 9 — Surah Al-Mujadila 58:9

Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan za ku yi ganawa, to, kada ku gana game da zunubi da zalunci da saɓa wa Manzon Allah, kuma ku yi ganawa game da alheri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda za a tattara ku zuwa gare, shi

Verse 10 — Surah Al-Mujadila 58:10

Ganawar daga Shaiɗan take kawai domin ya munana wa waɗanda suka yi imani, alhali kuwa ba zai iya cutar su da kome ba face da iznin Allah. Kuma sai muminai su dogara ga Allah

Verse 11 — Surah Al-Mujadila 58:11

Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan an ce muka, *"Ku yalwata a cikin majalisai," to, ku yalwata, sai Allah Ya yalwata muku, kuma idan an ce muku, "Ku tashi" to, ku tashi. Allah na ɗaukaka waɗanda suka yi imani daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajoji masu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kome

Verse 12 — Surah Al-Mujadila 58:12

Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan za ku ganawa da Manzon Allah, to, ku gabatar da 'yar sadaka* a gabanin ganawarku, wannan ne mafi alheri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sami (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 13 — Surah Al-Mujadila 58:13

Ashe, kun ji tsoron ku gabatar da sadakoki a gabanin ganawarku? To, idan ba ku aikata ba, kuma Allah Ya komo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi ɗa'a ga Allah da Manzon Sa. Kuma Allah ne Mai ƙididdigewa ga abin da kuke aikatawa

Verse 14 — Surah Al-Mujadila 58:14

Ashe, baka ga waɗanda* suka jiɓinci waɗansu mutane da Allah Ya yi hushi a kansu ba, ba su cikinku, kuma ba su a cikinsu kuma suna rantsuwa a kan ƙarya, alhali kuwa suna sane

Verse 15 — Surah Al-Mujadila 58:15

Allah Ya yi musu tattalin azaba mai tsanani. Lalle su abin da suka kasance suna aikatawa ya munana

Verse 16 — Surah Al-Mujadila 58:16

Sun riƙi rantsuwowinsu garkuwa, saboda haka suka kange (muminai) daga jihadin ɗaukaka tafarkin Allah. To, suna da azaba mai wulakantawa

Verse 17 — Surah Al-Mujadila 58:17

Dukiyoyinsu ba su wadatar musu kome ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan 'yan wuta ne. Su, masu dawwama ne a cikinta

Verse 18 — Surah Al-Mujadila 58:18

Ranar da Allah ke tayar da su gaba ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda suke yi muku rantsuwa (a nan duniya) kuma suna zaton cewa su a kan wani abu suke! To, lalle su, su ne maƙaryata

Verse 19 — Surah Al-Mujadila 58:19

Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, su ne masu hasara

Verse 20 — Surah Al-Mujadila 58:20

Lalle, waɗanda ke saɓa wa Allah da ManzonSa waɗannan suna a cikin (mutane) mafi ƙasƙanci

Verse 21 — Surah Al-Mujadila 58:21

Allah Ya rubuta cewa," Lalle zan rinjaya, Ni da Manzanni Na." Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwayi

Verse 22 — Surah Al-Mujadila 58:22

Ba za ka sami mutane masu yin imani da Allah da RanarLahira suna soyayya da wanda ya saɓa wa Allah da ManzonSa ba, ko da sun kasance ubanninsu ne, ko ɗiyansu ko 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu, kuma Ya ƙarfafa su da wani ruhi* daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah su ne masu babban rabo