Shi ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kafirta daga Mazowa Littafi,* daga gidajensu da kora** ta farko. Ba ku yi zaton suna fita ba, kuma sun tabbata cewa ganuwowinsu masu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya je musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jefa tsoro a cikin zukatansu, suna rushe gidajensu da hannayensu da kuma hannayen muminai. To, ku lura fa, ya masu basirori
Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganima ga Manzon Sa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawaki ko raƙuma ba amma Allah ne Ya rinjayar da Manzannin Sa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ikon yi ne a kan kome
Abin da Allah Ya sanya shi ganima ga Manzon Sa dagamutanen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na Manzon Sa ne kuma na masu dangantaka da marayu da miskinai da ɗan hanya* (matafiyi) ne domin kada ya kasance abin shawagi a tsakanin mawadata daga cikinku kuma abin da Manzo ya ba ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙuba ne
(Ku yi mamaki) Ga matalauta masu hijira waɗanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah da kuma yarda, kuma suna taimakon Allah da Manzon Sa! Waɗannan su ne masu gaskiya
Da waɗanda suka zaunar da gidajensu (ga Musulunci) kuma (suka zaɓi) imani, a gabanin zuwansu,* suna son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma ba su tunanin wata bukata a cikin ƙirazansu daga abin da aka bai wa muhajirina, kuma suna fifita waɗansu a kan kawunansu, kuma ko da suna da wata larura. Wanda ya saɓa wa rowar ransa, to, waɗannan su ne masu babban rabo
Kuma waɗanda suka zo daga bayansu, suna cewa, "Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin imani, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukatanmu ga waɗanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai
Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munafinci*ba, suna cewa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kafirta daga Mazowa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle za mu fita tare da ku, kuma ba za mu yi ɗa'a ga kowa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yaƙe ku, lalle za mu taimake ku haƙiƙatan?" Alhali kuwa Allah na shaidar cewa lalle su tabbas, maƙaryata ne
Lalle idan an fitar da su, ba za su fita tare da su ba kuma lalle idan an yaƙe su ba za su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙiƙatan, za su juyar da bayansu domin gudu, sa'an nan kuma ba za a taimake su ba
Ba su iya yaƙar ku gaba ɗaya, face a cikin garuruwa masu ganuwa da garuna, ko kuma daga bayan katangu. Yakinsu a tsakaninsu mai tsanani ne, kana zaton su a haɗe, alhali kuwa zukatansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa domin su, lalle wasu irin mutane ne da ba su hankalta
Kamar misalin Shaiɗan a lokacin da yake ce wa mutum, "Ka kafirta," To, a lokacin da ya kafirta ɗin, ya ce (masa): "Lalle babu ruwana da kai. Lalle ni ina tsoron Allah Ubangijin halitta
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa
Da Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dutse, da lalle ka ga dutsen yana mai tawali'u, mai tsattsagewa saboda tsoron Allah, kuma waɗancan misalai Muna bayyana su ne ga mutane, da fatan za su yi tunani
Shi ne Allah, wanda babu abin bautawa face shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarewa, Mabuwayi, Mai tastawa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi
Shi ne Allah, Mai halitta, Mai ginawa, Mai surantawa. Yana da sunaye masu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa suna tsarkake Shi, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima