Back to Languages

Hausa - Chapter 60 - Al-Mumtahanah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Mumtahanah 60:1

Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi maƙiyi Na kuma maƙiyinku masoyi, . Kuna jefa soyayya* zuwa gare su, alhali kuwa haƙiƙa sun kafirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, suna fitar da Manzon Allah tare da ku (daga gidajenku) domin kun yi imani da Allah, Ubangijinku, idan kun fito domin jihadi saboda ɗaukaka kalmaTa da neman yardaTa, kuna asirta soyayya zuwa gare su alhali kuwa Ni ne Mafi sani ga abin da kuka ɓoye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya

Verse 2 — Surah Al-Mumtahanah 60:2

Idan sun kama ku, za su kasance maƙiya a gare ku, kuma su shimfiɗa hannuwansu da harsunan gurin ku kafirta

Verse 3 — Surah Al-Mumtahanah 60:3

Zumuntarku ba za ta amfane ku ba, haka kuma ɗiyanku, a Ranar Kiyama. (Allah) zai* rarrabe tsakaninku, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatawa

Verse 4 — Surah Al-Mumtahanah 60:4

Lalle abin koyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrahim da waɗanda ke tare da shi a lokacin da suka ce wa mutnensu, "Lalle mu babu ruwanmu daku, kuma da abin da kuke bautawa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu, sai kun yi imani da Allah Shi kaɗai." Face maganar Ibrahim ga ubansa (da yace), "Lalle za ni nema maka gafara kuma ban mallaki kome ba daga Allah saboda kai." "Ya Ubangijinmu! A gare Ka muka dogara, kuma gare Ka muka mayar da al' amuranmu, kuma zuwa gare Ka makoma take

Verse 5 — Surah Al-Mumtahanah 60:5

Ya Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kafirta, kuma Ka yi gafara gare Mu. Ya Ubangijinmu! Kai ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 6 — Surah Al-Mumtahanah 60:6

Lalle, haƙiƙa, abin koyi mai kyau ya kasance a gare ku daga cikinsu, ga wanda ya kasance yana fatan (rahamar) Allah da Ranar Lahira, kuma wanda ya juya baya, to, lalle Allah, Shi ne wadatacce, Godadde

Verse 7 — Surah Al-Mumtahanah 60:7

Ana tsammanin Allah Ya sanya, a tsakaninku da tsakanin waɗanda kuka yi ƙiyayya da su, wata soyaya daga gare su, kuma Allah Mai ikon yi ne, kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 8 — Surah Al-Mumtahanah 60:8

Allah ba Ya hana ku, daga waɗanda ba su yaƙe ku ba saboda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidajenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu adalci. Lalle Allah Yana son masu adalci

Verse 9 — Surah Al-Mumtahanah 60:9

Allah Yana hana ku kawai daga waɗanda suka yake ku saboda addini kuma suka fitar da ku daga gidajenku, kuma suka taimaki juna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan su ne azzalumai

Verse 10 — Surah Al-Mumtahanah 60:10

Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan mata muminai suka zo muku, suna masu hijira, to, ku jarraba su. Allah Shi ne mafi sani ga imaninsu. To, idan kun san su muminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kafirai. Su matan ba su halatta ga aurensu, su kuma kafiran ba su halatta ga auren matan. Ku ba su abin da suka ɓatar na dukiya. Kuma babu laifi a kanku ga ku aure su idan kun ba su sadakokinsu. Kuma kada ku riƙe auren mata kafirai, kuma ku tambayi abin da kuka ɓatar daga dukiya, su kuma kafirai su tambayi abin da suka ɓatar na dukiya. Wannan hukuncin Allah ne Yana hukunci a tsakaninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima

Verse 11 — Surah Al-Mumtahanah 60:11

Kuma idan wani abu ya kuɓuce muku daga matanku zuwa ga kafirai sa'an nan kuma kuka ɗauki fansa, to, sai ku bai wa waɗanda matansu suka tafi kwatankwacin abin da suka ɓatar na dukiya. Kuma ku yi biyayya da taƙawa ga Allah wanda kuke masu imani da Shi, Shi Kaɗai

Verse 12 — Surah Al-Mumtahanah 60:12

Ya kai Annabi! Idan mata muminai suka zo maka suna yi maka mubaya'a a kan ba za su yi shirki da Allah ba ga kome, kuma ba su yin sata, kuma ba su yin zina, kuma ba su kashe,* ya'yansu, kuma ba su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirawa** a tsakanin hannuwansu da ƙafafunsu kuma ba su saɓa maka ga wani abu da aka sani na shari'a, to, ka karɓi mubaya'arsu, kuma ka nemi Allah Ya gafarta musu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 13 — Surah Al-Mumtahanah 60:13

Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku jiɓinci waɗansu mutane* da Allah Ya yi hushi a kansu. Lalle sun yanke tsammani daga (rahamar) Lahira, kamar yadda kafirai suka yanke tsammani daga mazowa** kaburbura