Kuma a lokacin da Musa ya ce wa mutanensa: "Ya mutanena! saboda me kuke cutar da ni, alhali kuwa lalle kun sani cewa lalle ni Manzon Alah ne zuwa gare ku?" To, a lokacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukatansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasiƙai
Kuma a lokacin da Isa ɗan Maryama ya ce: "Ya BaniIsra'ila! Lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bayar da bushara da wani Manzo da ke zuwa a bayana, Sunansa Ahmad (Mashayabo)." To, a lokacin da ya je musu da hujjoji, suka ce: "Wannan sihiri ne, bayyananne
Kuma wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhali kuwa shi, ana kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai
Ku yi imani da Allah da Manzon Sa, kuma ku yi jihadi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dukiyoyinku da rayukanku. Wannan shi ne alheri a gare ku idan kun kasance kuna da sani
Sai Allah Ya gafarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗakuna masu daɗi a cikin gidajen Aljannar zama. Wannan shi ne babban rabo, mai girma
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Isa ɗanMaryama ya ce ga Hawariyawa, "Waɗanne ne mataimakana zuwa ga (aikin) Allah?" Sai wata ƙungiya daga Bani Isra'ila ta yi imani, kuma wata ƙungiya ta kafirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi imani a kan maƙiyansu, saboda haka suka wayi gari marinjaya