Back to Languages

Hausa - Chapter 62 - Al-Jumuah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Jumuah 62:1

Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasa suna tasbihi ga Allah, Mamallaki, Mai tsarki' Mabuwayi, Mai hikima

Verse 2 — Surah Al-Jumuah 62:2

Shi ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'adu,* wani Manzo daga gare su yana karanta ayoyin Sa a kansu, kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su littafin da hikimarsa ko da yake sun kasance daga gabaninsa lalle suna a cikin ɓata bayyananna

Verse 3 — Surah Al-Jumuah 62:3

Da waɗansu mutane* daga gare su, ba su i da riskuwa da su ba, alhali kuwa shi ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 4 — Surah Al-Jumuah 62:4

Waccan wata falalar Allah ce Yana bayar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abucin dukan falala mai girma

Verse 5 — Surah Al-Jumuah 62:5

Misalin waɗanda aka ɗora wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misalin jaki ne Yana ɗaukar littattafai. Tir da misalin mutanen* nan da suka ƙaryata game da ayoyin Allah! Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai

Verse 6 — Surah Al-Jumuah 62:6

Ka ce: "Ya ku waɗanda suka tuba (Yahudu)! Idan kun riya cewa ku ne zaɓaɓɓun Allah ba sauran mutane ba, sai ku yi gurin mutuwa* idan kun kasance masu gaskiya

Verse 7 — Surah Al-Jumuah 62:7

Kuma ba za su yi gurinta ba har abada saboda abin da hannayen su suka gabatar. Kuma Allah ne masani ga azzalumai

Verse 8 — Surah Al-Jumuah 62:8

Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudu daga gareta, to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma ana mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, domin Ya baku labari game da abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 9 — Surah Al-Jumuah 62:9

Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan anyi kira zuwa ga salla a ranar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar* ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alheri a gare ku idan kun kasance kuna sani

Verse 10 — Surah Al-Jumuah 62:10

Sa'an nan idan an ƙare salla, Sai ku watsu a cikin ƙasa kuma ku nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci sunan Allah da yawa ɗammaninku, ku sami babban rabo

Verse 11 — Surah Al-Jumuah 62:11

Kuma idan suka ga wani fatauci ko kuma wani wasan shagala, sai su yi ruguguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kana tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah ne mafi alheri daga fataucin, alhali kuwa Allah ne Mafi alherin masu arzutawa