Idan munafukai* suka je maka suka ce: "Mune shaidar lalle kai haƙiƙa Manzon Allah ne," Kuma Allah Yana sane da lalle Kai, haƙiƙa Manzon Sa ne, kuma Allah Yana shaida lalle munafukan haƙiƙa, maƙaryata ne
Kuma idan ka gan su, sai jikunansu su ba ka sha'awa kuma idan sun faɗa,* za ka saurara ga maganarsu. Kamar dai su ƙyami ne wanda aka jingine. Suna zaton kowace tsawa a kansu take. Su ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Ya la'ane su. Yaya ake karkatar da su
Su ne waɗanda ke cewa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su watse," alhali kuwa taskokin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munafukai ba su fahimta
Suna cewa "Lalle ne idan mun koma* zuwa Madinar, haƙiƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhali kuwa rinjayar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da muminai, kuma amma munafikai ba su sani ba
Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: "Ya Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci domin in gaskata kuma in kasance daga salihai