Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa suna tasbihi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi godiya take. Kuma Shi, a kan kome, Mai ikon yi ne
Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙassai. Kuma Yana sanin abin da kuke boyewa da abin da kuke bayyanawa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙiraza
Wancan saboda lalle su Manzanninsu sun kasance suna je musu da hujjoji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mu?" Sai suka kafirta kuma suka juya baya, kuma Allah Ya wadatu (daga gare su). Kuma Allah wadatacce ne, Godadde
Waɗanda suka kafirta sun riya cewa ba za a tayar da su ba. Ka ce: "Ni, ina rantsuwa da Ubangijina. Lalle za a tayar da ku haƙiƙatan, sa'an nan kuma lalle ana ba ku labari game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne
A ranar da Yake tattara ku domin ranar taruwa. Wancan ne ranar kamunga. Kuma wanda ya yi imani da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa munanan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma
Wata masifa ba za ta samu ba face da iznin Allah. Kuma wanda ya yi imani da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kome, Masani ne
Ya ku waɗanda suka yi imani! Lalle ne daga matanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi* a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yafe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai
Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sami iko. Kuma ku saurara kuma ku yi ɗa'a, kuma ku ciyar, ya fi zama alheri gare ku. Kuma wandaya saɓa wa rowar ransa, to, waɗannan su ne masu babban rabo